An ƙirƙiro masarautun iyayen ƙasa biyu a Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Gwamantin jihar Kebbi ta amince da ƙirƙiro sababbin sarautun iyayen ƙasa biyu daga ƙaramar hukumar Argungu a cikin yankin masarautar Sarkin Kabin Argungu.

Sanarawar tana ƙunshe ne a cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu Honarabul Garba Umar Dutsinmari ranar Laraba ɗin nan.

Takardar ta ce ƙirƙiro masarautun iyayen ƙasar Gwazange da Yamman ya biyo bayan yanke shawarar akwai buƙatar ƙarin sarautun iyayen ƙasa a cikin ƙwaryar garin Argungu, ƙaramar hukumar mulki ta Argungu ta kuma amince da haka inda aka ɗaga darajar hakimin anguwar Gwazange Muhammadu Ibrahim zuwa Uban ƙasa yayin da aka ƙirƙiro yankin Yamman.
Haka-zalika an kuma amince da bayar da sarautar uban ƙasar Gwazange ga Muhammed Ibrahim sai Sarautar Yamman mai faɗa a Gungu ga Alhaji Abubakar Muhammad Mera.

Takardar ta bayyana cewa wannan ya yi daidai da kundin tsarin mulki na jihar Kebbi kan dokokin ƙananan hukumomi na 2008 sashe na 10 ƙaramin sashe na (A da B) wanda shi ne ya bai wa ƙananan hukumomi damar ƙirƙiro masarautun iyayen ƙasa.
Takardar ta bayyana cewa bayar da waɗannan sarautun ya biyo bayan la’akari da irin gudummawar da su ke bayarwa wajen cigaban al’umma a inda aka fito.
Daga ƙarshe an nemi sababbin sarakunan da su ji tsoron Allah wajen aiwatar da haƙƙin da Allah ya ɗora musu na jagoranci.

By ukarofi

Leave a Reply