
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’umma a yankin Gadar Apo na Abuja sun shiga firgici a daren Alhamis wayewar Juma’a bayan ɓullar rahotannin tarwatsewar wani abin fashewa a kusa da gidan man Shafa, kusa da Otel ɗin Rita Lori da ke Garki.
Wani shaida ya bayyana cewa ya ce ƙarar fashewar wani abu a lokuta mabambanta har sau bakwai, inda da fari ya yi zaton ko bom ne.
An ruwaito cewa al’amarin ya faru ne a kuaa da gidan man, wanda ke haɗa jama’a, lamarin da ya haifar da tsoro da tilasta wa masi ababen hawa da mazauna yankin tserewa domin neman tsira da rayuwarsu.
Daga bisani jami’an hukumomin kashe gobara ta tarayya da ta Abuja sun garzaya yankin domin bayar da agajin gaggawa tare da ƙoƙarin kashe wutar don kada ta bazu zuwa wasu yankuna.
A yayin haɗa wannan rahoto, ba a tabbatar da ainihin abin da ya sabbaba faruwar al’amarin ba a hukumance da kuma matakin damejin da ya haddasa.
Jami’an hukumomin tsaro sun cigaba da kasancewa a yankin tare da shawartar jama’a da su ƙaurace wa yankin.
