Rikicin shugabanci: An halaka ‘yan majalisar shurar ISWAP huɗu

Spread the love

Rikicin shugabanci acikin ƙungiyar ISWAP na ƙara tsananta biyo bayan wani sabon rahoton sirri da ke nuna cewa an kashe mambobi huɗu na Majalisar Shura ta ƙungiyar.

A cewar wani rahoton sirri daga Zagazola Makama, mambobin guda huɗu, waɗanda aka garkame su a makon da ya gabata ta hannun dakarun ISWAP, an ce wani babban jami’in ISWAP mai suna Ba Shuwa ne ya kashe su a maɓoyarsu ta Kwatan Dila a ranar Laraba, 6 ga Agusta.

Wannan sabon al’amari ana kyautata zaton zai ƙara bayyana ƙaruwar rashin jituwa a tsakanin ‘ya’yan ƙungiyar da kuma samun rarrabuwar kawuna a cikinta wanda hakan haddasa tsattsagewar ta a yankin Tafkin Chadi.

Rahotanni sun a bayyana cewa, mambobin majalisar huɗu an kama su ne a tsakiyar rikicin shugabanci da ake cigaba da yi acikin ISWAP, kodayake ba a samu damar tabbatar da takamaiman zarge-zargen da ake musu ba.

Wara majiya mai tushe ta leƙen asiri ta ce kisan da aka musu daga baya ya ƙara haifar da fargabar cewa ana tsaftace tawagar dakarun cikin gida tare da ƙarfafa iko da shugabanni masu adawa ke yi a cikin ƙungiyar.

Wannan ci-gaba na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan ta’adda ake fuskantar ƙaruwar samamen soja da ke ɗaiɗaita tsarin shugabancin ‘yan ta’adda shiyyar musamman idan sauran manyan kwamandoji da mambobin majalisar shurar suka fassara kisan a matsayin wani ɓangare na tsaftace shugabancinsu.

A al’adance, majalisar na taka muhimmiyar rawa a tsarin yanke shawara na ƙungiyoyin ta’addanci, ciki har da batutuwan da suka shafi shugabanci, gudanar da ayyuka, gudanarwa da kuma sarrafa albarkatu.

By Babaji

Leave a Reply