
Daga BELLO A BABAJI a Abuja
Sanatan da ke wakiltar Osun ta Gabas, Francis Fadahunsi, ya samu beli daga hannun rundunar ‘yan sandan jihar bayan bincikensa akan kalamansa da suka tayar da hazo na “kill Accord” ajihar.
A wani bidiyo da aka wallafa a kafar X a ranar Talata, an ga yadda sanatan APCn ke magana cikin harshen Yarabanci, inda ya kirayi magoya bayansa da su halaka mambobin jam’iyyar Accord Party (AP).
Saidai daga bisani ya gaggauta kare kalaman nasa bayan sun tayar da ƙura a kafafen sada zumunta, inda ya ce an fassara su ta wata hanya.
A cewarsa, yana ƙoƙarin warware matsalolin zargin “kashe mambobin APC ne a garin Ilesa daga wasu ɓata-gari kuma yana cewa jam’iyyarsa za ta bayar da kariya ga mutanenta matuƙar aka cigaba da aikata musu ta’addanci.
“Bidiyon aka yi wa kwaskwarima da gangan kan ainihin abin da na faɗa. Abin da na ce shi ne idan zargin kashe mambobinmu daga ɓata-garin Accord Party bai dakata ba, jam’iyyarmu za ta mayar da martani. Ina magana ne akan cigaba da aukuwar rikicin da oe faruwa daga maharan da ke farmakin mambobinmu a Ilesa da wasu sassan jihar,” inji Sanatan.
A ranar Laraba ne Sanata Fadahunsi ya ziyarci ofishin Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) a Osogbo da misalin ƙarfe 2 na rana bayan rundunar ‘yan sanda ta gayyace shi a hukumance kan kalaman nasa da suka karaɗe kafafen sadarwa.
Daga bisani, Kakakin rundunar, Abiodun Ojelabi ya tabbatar wa jaridar TheCable cewa an bayar da belin sanatan, yayin da kuma za a cigaba da aiki a kai domin gano ainihin haƙiƙanin al’amari.
