Gwamnatin Kebbi ta raba wa makarantun gaba da sakandare motoci

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Gwamna Malam Nasir Idris ya raba wa makarantun gaba da sakandare mallakar jihar Kebbi guda bakwai da ke faɗin jihar manyan motoci ƙirar Bas-bas.

Da ya ke jawabi yayin ƙaddamar da motocin a gidan Gwamnatin jihar da ke Birnin Kebbi ranar Laraba ɗin nan, gwamna Nasir Idris ya ce wannan ya biyo bayan la’akari da akwai buƙatar motoci musamman ga ɗalibai don ƙara saukaka musu zirga-zirga daga makarantu zuwa wajen kwana musamman waɗanda ke zama a cikin gari da ke da nisa da makarantu.

Ya ce yana fata hukumomin makarantun za su riƙe motocin tare da ba su kulawa ta musamman wajen amfani da su.

Ya ce a matsayin sa na Malami ya zama wajibi ya kare martabar makarantu da ɗalibai wanda yana daga cikin alƙawurran sa a lokacin yaƙin neman zaɓe.

Da ya ke jawabi, Kwamishinan Ilmi na jihar Alhaji Isah Abubakar Tunga, ya yaba wa gwamna Nasir Idris bisa ga cika alƙawurran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe tare da ba shi tabbacin ba su cikakkiyar kulawa a ƙarƙashin hukumar Ilmi.
Ya kuma yaba wa gwamnan bisa ga kulawar da ya ke bai wa fannin ilmi inda ya ce a duk lokacin da wannan hukumar ta zo da wata buƙata ya kan duba tare da aiwatar da buƙatar cikin lokaci.

Makarantun da suka sami motocin dai sun haɗa da kwalejin Ilmi ta Adamu Augie Argungu, Kauran Gwandu College of Nursing and Midwifery Sciences, Ambursa, College of Health Sciences and Technology, Jega, Abdullahi Fodio University of Science and Technology, Aliero, College of Advanced and Legal Studies, Yauri, College of Nursing Sciences, Birnin Kebbi, Kebbi State Polytechnic, Dakingari.

By ukarofi

Leave a Reply