2027: Atiku ya maka Tinubu a kotu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya maka Shugaba Bola Ahmed Tinubu a gaban Babbar Kotun Tarayya, inda yake ƙalubalantar cancantarsa ta tsaya wa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 da ke tafe.

Atiku ya kuma buƙaci kotun da ta fayyace bayani akan ko Shugaba Tinubu da jam’iyyarsa APC, sun cancanci a soke cancantarsu ta shiga zaɓen.

Haka kuma, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya zayyano Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a matsayin ɗaya daga cikin masu kare ƙarar.

Daga cikin ababen da Atiku yake ƙorafi akansu akwai zargin yin amfani da jabun takardar shaidar kammala aikin yi wa ƙasa hidima ta NYSC.

Sannan, ya nemi kotun da ta hana Tinubu tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, kamar yadda ya bayyana a ƙarar, wadda ya shigar a ranar Juma’a.

Atiku ya dogara ne da zargin cewa an ƙirƙiro ko kuma an yi amfani da takardar shaidar NYSC da ake danganta wa Shugaba Tinubu, inda yake neman kotu ta ɗauki matakin da ya dace kan cancantarsa ta shiga zaɓen na 2027.

By Babaji

Leave a Reply