
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Malaman jami’a da suka haɗa da masu muƙamin farfesa da wasu sama da guda 200 ne suka bar Jami’ar Kaduna KASU, bisa rashin ingancin lamuran gudanarwa da rashin aiwatar da yarjejeniyar Gwamnatin Tarayya da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta 2025, inji reshen ƙungiyar na KASU.
Rahotanni sun bayyana cewa ASUU reshen KASU ta bayar da wa’adin sati biyu ga hukumomin jami’o’i da sauran masu ruwa da tsaki da su fara aiwatar da yarjejeniyar yadda aka tsara ta, tana mai gargaɗin cewa rashin yin hakan ka iya haifar da yajiin aikin sai baba-ta-gani a jami’ar.
Shugaban ASUU-KASU, Abubakar Abdullahi ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin hira da manema labarai da aka gudanar a sakatariyar ƙungiyar da ke farfajiyar jami’ar a Kaduna.
Abdullahi ya bayyana cewa, yarjejeniyar FGN-ASUU, wadda ta shar’ɗanta inganta yanayin aiki ga malaman jami’o’in Nijeriya, ta fara aiki ne tun a watan Junairun 2026, amma ba a aiwatar da ita ba a KASU.
A cewarsa, ƙungiyar ta rubuta wasiƙu da dama kan al’amarin ga hukumar gudanarwar jami’ar, majalisar shugabanci da shugaban jami’ar da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, inda aka kiraye su da su ƙoƙarta wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar bisa yadda dokar jami’ar ta tanada.
Saidai, duk da cewa tun tsawon watanni takwas da sanya wa yarjejeniyar hannu, har zuwa yanzu ba ta fara aiki ba a KASU yayin da jami’o’i da dama suka aiwatar da ita, yana mai cewa cigaba da jinkiri ka iya haddasa biyan jimillar albashin da malaman suke bi tun daga Junairu, 2026.
