Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Majalisar Zartarwar Tarayya (FEC) ta amince da yin gyara ga Dokar Lafiyar ƙwaƙwalwa ta ƙasa domin cire yunƙurin kashe kai daga cikin laifukan da doka ke hukuntawa a Nijeriya.
Ministan Lafiya da Jinƙai, Farfesa Ali Pate, ne ya bayyana hakan bayan taron FEC da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a Abuja ranar Laraba.
Ya ce ƙudirin gyaran dokar, wanda za a miƙa wa Majalisar ƙasa domin ta yi masa duba da kuma zartar da shi, zai sauya yadda ake kallon mutanen da suka yi yunƙurin kashe kansu, daga hukunta su zuwa ba su kulawa, kariya da tallafin da suka dace.
Farfesa Pate ya bayyana cewa har yanzu yunƙurin kashe kai na cikin laifukan da dokokin Criminal Code da Penal Code da aka gada daga zamanin mulkin mallaka suka tanada, duk da cewa Dokar Lafiyar ƙwaƙwalwa ta ƙasa ta 2021 ta tanadi kulawa da kariya ga mutanen da ke cikin haɗarin cutar da kansu.
Ya ce wannan tsarin na hukunta yunƙurin kashe kai na iya hana mutane neman taimakon likitoci ko sauran hanyoyin samun kulawa, tare da haifar da rashin daidaito tsakanin tsoffin dokokin laifi da manufofin ƙasar kan lafiyar ƙwaƙwalwa.
Ministan ya ce an cimma matsayar gyaran dokar ne bayan shawarwari tsakanin Ma’aikatun Lafiya da Jinƙai da na Shari’a, masu fafutukar inganta lafiyar ƙwaƙwalwa, Ofishin Antoni-Janar na Tarayya, kwamitin musamman da Majalisar Wakilai.
Ya bayyana cewa wani kwamiti ne aka kafa bayan wani kuduri daga Majalisar Wakilai domin duba batun da kuma samar da gyaran da ya dace ga dokar.
A cewar Pate, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kiyasta cewa kashe kai na haddasa mutuwar sama da mutane 7,000 a Nijeriya a duk shekara, yayin da ake kuma samun kimanin yunƙurin kashe kai 300,000 a shekara.
A wani ɓangare na taron, FEC ta kuma amince da Kudirin Dokar Kafa Cibiyar Kiwon Lafiyar Baki ta ƙasa ta 2026, wanda za a miƙa wa Majalisar ƙasa domin tabbatar da shi.
Ministan ya ce cibiyar za ta kasance babbar cibiyar kula da marasa lafiya, bincike da horaswa a fannin lafiyar baki, tare da samar da tsarin doka da na hukumomi domin yaƙi da cututtukan baki da sauran matsalolin da suka shafi lafiyar baki.
FEC ta kuma amince da wasu manyan ayyukan inganta ababen more rayuwa a Asibitin ƙasa da ke Abuja, waɗanda suka haɗa da ginin ofishin gudanarwa na Naira miliyan 18.74, asibitocin zamani da rukunin ɗakin tiyata na Naira biliyan 64.92, wani babban ɓangare na asibiti na Naira biliyan 103 da kuma Cibiyar Kula da Cututtukan ƙwaƙwalwa da Jijiyoyin ƙwaƙwalwa ta Naira biliyan 69.
Pate ya ce Cibiyar Kula da Cututtukan ƙwaƙwalwa za ta samar da wuraren gudanar da tiyatar ƙwaƙwalwa, binciken hoton jiki, ayyukan jinya na musamman da kuma gyaran jiki ga masu fama da shanyewar barin jiki, ciwace-ciwacen ƙwaƙwalwa da sauran cututtukan jijiyoyin ƙwaƙwalwa.
Haka kuma, FEC ta amince da ware Naira biliyan 302.3 domin tsarawa, ginawa, samar da kayan aiki, kulawa da kuma kammala Cibiyar Nazari da Maganin Ciwon Daji ta ƙasa (NICRAT), wadda ake sa ran za a kammala cikin watanni 36.
Ministan ya ce cibiyar za ta zama babbar cibiyar bincike, magani, kirkire-kirkire da horaswa kan cutar daji a Nijeriya.
Ya bayyana cewa an riga an kammala kuma aka ƙaddamar da wasu cibiyoyin kula da cutar daji da aka inganta a Katsina, Benin da Enugu.
Pate ya ce dukkan ayyukan za a gudanar da su ne bisa kasafin kuɗin hukumomin da abin ya shafa, tare da bin ƙa’idojin sayayya na gwamnati da kuma samun izinin Hukumar Kula da Ayyukan Saye ta ƙasa (BPP).
Ya ce zuba jari a ababen more rayuwar kiwon lafiya zai inganta ayyukan kiwon lafiya, samar da kyakkyawan yanayin aiki ga ma’aikatan lafiya da kuma rage yawan ƙwararrun likitocin Nijeriya da ke barin ƙasar domin neman ingantattun damar aiki a ƙasashen waje.
