Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina ya amince da naɗin Masa’ud Al’mustapha Banye a matsayin shugaban ma’aikata na riƙo a Jihar Katsina.
Naɗa Masa’ud ya biyo bayan ajiye aikin da tsohon shugaban ma’aikata Alhaji Falalu Bawale bayan ya shafe shekara 35 a aikin gwamnatin Jihar.
A wata takardar sanarwa ɗauke da sanya hannun sakataran gwamnati Barista Abdullahi Garba Faskari,ya bayyana naɗin a wani ƙoƙari na inganta aikin gwamnati da zai daidaita da shirin gwamnatin Dikko Raɗɗa na ‘RENEWED HOPE’.
Abdullahi Faskari ya taya Masa’ud Banye murnar samun wannan muka tare da kira a gare shi da ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen kawo cigaba a aikin gwamnati.
Kafin naɗin nasa, Masa’ud Al’mustapha Banye shine babban sakatare a ma’aikatan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu a Jihar.
