Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Mataimakin gwamnan jihar Katsina, Faruk Joɓe, ya ce a lokacin da gwamnatin Dikko Radda ta kama aiki a shekarar 2023, hare-haren ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro sun yi ƙamari a kusan ƙananan hukumomi 26 daga cikin 34 na jihar.
Jobe ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da yake wakiltar gwamna Radda a taron rubu’i na biyu na shekarar 2026 na daraktocin hukumomin tsaro na jihohin Arewa maso Yamma wanda aka gudanar a shalkwatar hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) da ke Katsina.
Taron, mai taken “Haɗa Kai Don Yaƙar Ta’addanci”, ya haɗa da daraktocin SSS da sauran jami’an tsaro daga jihohin Arewa maso Yamma domin tattauna matsalolin ta’addanci, ‘yan bindiga, satar mutane da sauran barazanar tsaro da ke addabar yankin.
An samu sauyi mai yawa a fannin tsaro:
Jobe ya ce yanayin tsaro a Katsina ya “inganta matuƙa” tun bayan da gwamnatin Radda ta hau kan mulki a 2023.
Ya danganta ci gaban da aka samu da haɗin guiwar matakan soji da amfani da tsarin sulhu ciki har da aiki tare da hukumomin tsaro na yau da kullum, shirye-shiryen tsaron al’umma da kuma wasu tsare-tsaren gwamnati.
Mataimakin gwamnan ya kuma buƙaci masu ruwa da tsaki su yi amfani da dabarun sadarwa wajen yaƙi da ta’addanci tare da kira ga kafafen yaɗa labarai da su riƙa taka-tsantsan wajen rahoton abubuwan da suka shafi tsaro.
Ya yi magana kan karuwar aikin jarida, inda ya yi gargaɗin cewa yaɗa bayanai ba tare da kula ba na iya haifar da matsaloli.
Sai dai bayanan da aka samu daga taron ba su fayyace irin dabarun yaɗa farfaganda da ake nufi da an yi amfani da su ba ko a matsayin dabara ta yaƙi da saƙonnin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, gyara bayanan da aka yi ƙarin gishiri a kansu ko kuma rage yaɗa bayanan hare-haren da aka tabbatar.
Jaridar The Guardian ta rawaito Jobe yana cewa lokacin da gwamnatin ta kama aiki, “muna da kusan ƙananan hukumomi 26 da ake kai wa hare-hare a-kai-a-kai.”
Ya ce a wancan lokacin ana kashewa da satar mutane domin neman kuɗin fansa da sauran laifuka masu nasaba da rashin tsaro sun yadu a jihar, amma gwamnatin ta ce ta samu gagarumin ci gaba wajen magance waɗannan matsaloli.
Adadin ƙananan hukumomi 26 ya zama wani sabon ma’auni wajen tantance iƙirarin gwamnatin kan inganta tsaro duk da cewa hukumomin Katsina sun taɓa amfani da hanyoyi daban-daban wajen bayyana wuraren da matsalar rashin tsaro ya fi ƙamari.
A watan Janairun 2026, wata sanarwa da gwamnatin jihar fitar, ta ce, ƙananan hukumomi 19 ne ake ɗauka a matsayin yankunan da ‘yan bindiga ke ci gaba da kai hare-haren da satar mutane kafin zaɓen 2023.
A baya-bayan nan kuma, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Nasiru Mu’azu Danmusa, ya ce an raba ƙananan hukumomin jihar 34 zuwa yankuna takwas da ke kan gaba wajen fuskantar hare-hare, 11 masu rauni da 15 da ba sa fama da wani rikici, domin saukaka tura jami’an tsaro da kayan aiki.
Duk da iƙirarin gwamnatin na cewa tsaro ya inganta, hare-haren ‘yan bindiga na ci gaba da faruwa a wasu sassan Katsina, musamman a ƙaramar hukumar Bakori.
A ranar 3 ga watan Agusta, Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa ‘yan bindiga sun kashe mutum ɗaya, sun jikkata aƙalla mutane bakwai tare da yin garkuwa da wasu 32 a ƙauyen Shuwaki.
Haka kuma a ranar Alhamis, Daily Trust ta ruwaito wani sabon hari a Unguwar Aminu da ke mazaɓar Kandarawa, inda aka ce an kashe mutane biyu, an jikkata huɗu da aka yin garkuwa da wasu shida.
Sai dai Blueprint Manhaja ba ta samu damar tantance waɗannan alƙaluma da kanta ba.
Jobe ya ce matakan da ba na soja ba da gwamnatin ta ɗauka sun haɗa da bayar da magani kyauta ga waɗanda hare-haren ‘yan bindiga ya rutsa da su da kuma zuba jari a harkar noma.
Ya ce gwamnatin ta kuma mayar da hankali kan bunkasa aikin gona ta hanyar samar da injinan noma, ingantattun iri, takin zamani da ayyukan jami’an faɗaɗa aikin gona.
A cewarsa, gwamnati ta ɗauki ma’aikatan fadada aikin gona 772 tare da horas da su, idan aka kwatanta da 78 kacal da ake da su shekarar 2023.
Daraktan SSS na Katsina, Alhassan Iliasu, ya ce taron zai ba hukumomin leken asiri na jihohin Arewa maso Yamma damar duba ƙalubalen tsaro da ke addabar yankin tare da samar da dabarun haɗin gwuiwa wajen yaƙi da ta’addanci.
Ya ce tattaunawar da aka gudanar za ta ba da damar fitar da jawabin bayan taro wanda zai zama jagora wajen yaƙi da ‘yan bindiga, satar mutane da sauran laifukan da ke da alaƙa da rashin tsaro.
Shugaban Daraktocin Tsaro na jihohin Arewa maso Yamma, Hussaini Abubakar, ya ce taron zai karfafa haɗin gwuiwa da musayar bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro.
Shi ma Kwamandan Burgediya ta 17 na Rundunar Sojin Nijeriya, Ishaya Ibrahim, ya jaddada muhimmancin samar da sahihan bayanan sirri da kuma kyakkyawan tsarin haɗin gwuiwa wajen gudanar da ayyukan tsaro.
Kwamishinan ’Yan Sandan Katsina, Aliyu Fage, ya ce rundunar ’yan sanda da SSS na ci gaba da musayar bayanan sirri domin inganta irin martanin da suke yi ga barazanar tsaro a jihar..
