Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Farfesa Isma’ila A Mungadi shugaban riƙo na jami’ar kimiyya da fasaha ta Abdullahi Fodiyo da ke Aliero ya ajiye aiki bayan watanni uku da naɗa shi.
Wannan bayanin yana ƙunshe ne a cikin wata takarda da ya gabatar wa hukumar makarantar ranar Juma’a 28, ga watan Agusta na wannan shekarar.
A cikin takardar, Mungadi ya bayyana cewa ajiye aikin ya biyo bayan rashin samun damar aiwatar da ayyukan da ya kamata a aiwatar bisa ƙa’idojin makarantar daga waɗansu ɓangarori.
Ya ce ya karɓi wannan aikin ne bisa ga zummar gyara taɓargazar da ta faru a baya da kuma ɗora sabon tubalin cigaba mai ɗorewa don dawo da martabar wannan makarantar da kuma tsarin shugabanci nagari.
Ya ƙara da cewa a maimakon haka sai dai tun lokacin da ya shiga ofis din ya soma cin karo da akasin haka inda ya yi ta ƙoƙarin kawo gyaran daga ƙarshe dai abin ya ci tura shi kuma ya yanke shawarar ajiye aikin.
“Idan dai ba ba zan iya gudanar da yin abinda ya kamata ba bisa ga wannan matsayin da aka ba ni ba na ganin na kawo tsari don cigaba ba to ban ga dalilin da zai sa na cigaba da riƙe muƙamin ba.” Inji shi
Mungadi ya yaba wa gwamnan jihar Kebbi Malam Nasir Idris bisa ga ganin cancantar sa kuma aka zaƙulo shi daga cikin mutane da dama da suka nemi wannan muƙamin.
Naɗin Mungadi ya biyo bayan rushe jagorancin makarantar sanadiyyar badaƙaloli daban-daban da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa na wani lokaci mai tsawo da gwamnatin jihar ta yi ƙoƙarin shawo kan su amma abin ya ci tura.
