
Ƙungiyar Direbobi ta Ƙasa (NURTW) ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, bisa yadda take ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta harkokin sufuri da samar da ababen more rayuwa a jihar.
Ƙungiyar ta ba Gwamna Lawal lambar yabo ta Ƙwarewa da Nagarta, wato Award of Excellence, a wani biki da aka gudanar ranar Laraba a Dome Pavilion da ke harabar Gidan Gwamnatin Jihar Zamfara a Gusau.
Baya ga karramawar, ƙungiyar ta kuma bayyana goyon bayanta ga Gwamna Lawal, inda ta amince da ya sake neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027.
Mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce Shugaban Kwamitin Amintattu na NURTW, Dakta Najeem Usman Yasin, ne ya jagoranci tawagar manyan jami’an ƙungiyar zuwa Gusau.
Tawagar ta ƙunshi Shugaban Ƙangiyar na Ƙasa, Musiliu Ayinde Akinsanya, wanda aka fi sani da MC Oluomo, da sauran manyan jami’an ƙungiyar.
Da yake jawabi, Gwamna Lawal ya ce amincewar NURTW da shi domin sake tsayawa takara ta nuna cewa haɗin gwiwar da ke tsakanin ɓangaren sufuri da gwamnatin jihar na haifar da sakamako mai kyau.
Gwamnan ya bayyana farin cikinsa da dawowar Dakta Najeem Usman Yasin, wanda yake riƙe da sarautar Makaman Gusau, yana mai cewa shi ne mutum na farko da ya zama Shugaban NURTW na Jihar Zamfara bayan shekarar 1996.
Ya ce dawowar Yasin na da muhimmiyar ma’ana saboda kasancewarsa wanda ya kafa tushen ƙungiyar ma’aikatan sufuri a Zamfara, yana mai cewa jihar na alfahari da irin gadon da ya bari.
Gwamna Lawal ya kuma yaba wa Shugaban NURTW na ƙasa, Musiliu Ayinde Akinsanya, da tawagar gudanarwar ƙungiyar bisa kokarinsu na sake fasalin tsarin ƙungiyar da kuma ƙara ƙwarewa a harkar sufuri a faɗin Nijeriya.
Ya ce karramawar da aka yi masa a wannan rana guda biyu ce, inda ta farko ita ce lambar yabo ta ƙwarewa da nagarta, wadda ya ce zai ɗauke ta a matsayin shaida kan irin ayyukan da gwamnatinsa ke yi da kuma ƙarin ƙwarin gwiwar yin abubuwa fiye da haka.
Ya ce karramawa ta biyu ita ce amincewar NURTW da ya sake tsayawa takara, yana mai bayyana ƙungiyar a matsayin ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin da ke da ƙarfi a matakin al’umma.
A cewarsa, wannan mataki na NURTW ya tabbatar masa da cewa manufofin gwamnatinsa na samun tasiri kai tsaye a rayuwar talakawan jihar.
Gwamna Lawal ya ce lokacin da gwamnatinsa ta karɓi ragamar mulkin Zamfara, ta yi alkawarin farfaɗo da jihar, tare da sanin cewa ingantaccen tsarin sufuri mai aminci yana daga cikin muhimman ginshiƙan bunƙasar tattalin arziki.
Ya bayyana cewa a wani mataki na cika wannan buri, gwamnatin ta raba motocin sufuri na jama’a guda 50 ga mambobin NURTW a farashi mai rangwame, domin taimaka musu wajen inganta rayuwarsu tare da sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a.
Gwamnan ya kuma ce gwamnatin ta gudanar da babban aikin gyaran Sakatariyar Majalisar NURTW ta Jihar Zamfara, domin samar wa ma’aikatan sufuri muhalli mai kyau da mutunci wajen gudanar da ayyukansu.
Tun da farko, Shugaban Kwamitin Amintattu na NURTW, Dakta Najeem Usman Yasin, ya ce shugabancin ƙungiyar ya lura da irin sauye-sauyen da Gwamna Dauda Lawal ya samu a Zamfara cikin shekaru uku da ya yi yana kan mulki.
Yasin ya ce zuwansu Gusau ya kasance ne domin nuna godiya ga gwamnan bisa ayyukan da ya gudanar, musamman ta hanyar ba shi lambar yabo ta ƙwarewa da nagarta.
Ya ce a matsayinsu na shugabannin ƙungiyar, wajibi ne su ware lokaci domin zuwa Zamfara tare da bayyana wa duniya irin ci gaban da suka ga gwamnan ya samu a jihar.
Yasin ya ƙara da cewa, zuwa ranar 1 ga Oktoban 2026, Zamfara za ta cika shekaru 30 da kafuwa, yana mai bayyana Gwamna Lawal a matsayin wata babbar baiwa da jihar ta samu.
A cewarsa, sauye-sauyen da Lawal ya samu cikin shekaru uku sun kai Zamfara wani mataki da ya yi daidai da ƙa’idojin duniya.
Ya ce saboda haka, a madadin NURTW, yana bayyana cikakken goyon bayan ƙungiyar ga Gwamna Dauda Lawal domin ya sake lashe zaɓen gwamna a 2027.
Yasin ya kuma yi kira ga dukkan mambobin ƙungiyar da su mara wa Gwamna Lawal baya tare da yin aiki domin ganin ya samu nasarar sake komawa kan kujerar gwamnan jihar a zaɓen 2027, domin ci gaba da ayyukan da ya fara.






