Hukuma ta maka Matatar Dangote kotu kan inganci da ayyukan dakon mai

Spread the love

Daga NAHDI MUSA MUHAMMAD

Kwanaki ƙalilan bayan kammala sanar da sayar da hannun jarin matatar Dangote ga jama’a ta hanyar IPO, sabuwar taƙaddama ta kunno kai tsakanin matatar da Hukumar Kula da Harkokin Haƙowa da Tace Albarkatun Man Fetur ta Nijeriya (NMDPRA), inda ɓangarorin biyu suka tsinci kansu a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Legas kan inganci da rarraba iskar gas ta propane, da kuma dakatar da ayyukan lodin kayayyakin mai a kan manyan motoci.

Taƙaddamar ta ƙara tsananta ne bayan NMDPRA ta umarci dakatar da lodin propane da fitar da shi ta manyan motoci daga matatar Dangote, matakin da matatar ta garzaya kotu domin ƙalubalantawa, tana zargin hukumar da yin amfani da ikonta ba bisa ƙa’ida ba.

A ranar 31 ga watan Agusta ne kotun ta bayar da umarnin wucin gadi da ya hana NMDPRA, jami’anta, wakilanta ko masu yi mata aiki shiga matatar, rufe ta, dakatar da aikinta, taƙaita shiga cikinta, tare da hana duk wani mataki da zai kawo cikas ga ayyukan matatar, har sai an saurari kuma an yanke hukunci kan babban ƙarar da ke gabanta.

A zaman kotun da aka yi ranar Laraba, lauyan NMDPRA, Matthew Burkaa, ya roƙi kotun da ta soke umarnin wucin gadin, yana mai cewa an samu wannan umarni ne ta hanyar gabatar da wasu bayanai da ba su dace ba tare da ɓoye wasu muhimman bayanai daga kotun.

Hukumar ta kuma ƙalubalanci ikon Mai Shari’a Akintayo Aluko na bayar da umarnin, tana mai cewa matatar Dangote ba ta gabatar da takardar sanarwar shari’a da doka ta tanada ba a lokacin da ta nemi kotun ta bayar da umarnin ba tare da jin ɗayan ɓangaren ba.

NMDPRA ta ce matakin dakatar da lodin propane da fitar da shi ta manyan motoci ya biyo bayan gano wasu abubuwa da take zargin sun haɗa da karkatar da motocin da ke ɗauke da propane zuwa hannun wasu kwastomomi da ba a san ko su waye ba kuma ba su da lasisin karɓar kayayyakin, da kuma zargin haca propane da sauran iskar gas a wasu masana’antun LPG.

Hukumar ta ce, ta fara binciken ne bayan gwaje-gwajen ɗakin gwaje-gwaje da aka yi kan samfurorin LPG daga masana’antu uku — Selai, Tewa da Ameego Pago — sun nuna cewa adadin propane da ke cikin kayayyakin ya haura kashi 50 cikin 100.

A cewar NMDPRA, ƙa’idar masana’antar man fetur ta tanadi cewa propane bai kamata ya wuce kashi 20 cikin 100 na hadin LPG ba, yayin da butane ya kamata ya kai kusan kashi 80 cikin 100.

Hukumar ta ce, ta gayyaci wakilan waɗannan masana’antu uku domin tattauna sakamakon gwajin, inda suka nuna kamfanin Sublime Oil and Gas Limited a matsayin wanda suke karɓar propane daga gare shi. Kamfanin na daga cikin masu sayen propane daga matatar Dangote.

Wannan ne ya sa NMDPRA ta faɗaɗa bincikenta, inda ta fara bibiyar bayanan samar da propane da kuma yadda ake haɗa shi a masana’antun LPG.

Hukumar ta kuma yi zargin cewa jami’anta sun fuskanci hana su shiga lokacin da suka je matatar Dangote a ranar 24 ga Agusta domin duba yadda ake lodin propane da kuma bayanan da suka shafi wannan aiki.

Daga bisani, NMDPRA ta aika wa matatar sanarwar yiwuwar saba wa ƙa’idoji, tare da umartar ta da ta dakatar da lodin propane da fitar da shi ta manyan motoci har sai an kammala binciken da kuma aiwatar da wasu ƙarin matakan tsaro.

Hukumar ta ce, binciken bayanan motocin da suka fitar da kaya daga matatar ya nuna wasu manyan saɓani. Ta yi zargin cewa kamfanin Sublime Oil and Gas ya ɗauki manyan motoci 25 ɗauke da propane a ranakun 20 da 22 ga Agusta domin kai su Naɓgas/Agasco, amma Naɓgas ya tabbatar da cewa motocin kaya shida ne kawai suka isa wurinsa. Hakan ya sa hukumar ta ce ba a san inda motocin 19 ɗin da suka rage suka shiga ba.

NMDPRA ta kuma ce bayanan da ta samu daga Jihar Delta sun nuna cewa wani kamfanin da ke karɓar propane daga matatar ya ɗauki manyan motoci 52 tsakanin watan Mayu da Agusta 2026 domin kai su Navgas, amma Navgas ya tabbatar da cewa babu ko guda ɗaya daga cikin waɗannan kayan da ya isa wurinsa.

By ukarofi

Leave a Reply