DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya
Matar gwamnan jihar Nasarawa Hajiya Salifat Abdullahi Sule tayi kira na musamman ga ƙungiyar ‘yan jarida mata ta Najeriya wato NAWOJ da su rike ƙa’idojin sana’ar jarida da gaskiya domin cigaban al’umma.
Hajiya Salifat Sule ta bayyana haka ne a birnin Lafia a lokacin taron da aka gudanar domin bikin cika shekara ɗaya na sabbin shugabannin ƙungiyar ta NAWOJ reshen jihar Nasarawa da kuma ƙaddamar da littafin Compendium of Nasarawa Amazons’’ a turance.
Matar gwamnan ta kuma bayyana aniyarta ta cigaba da tallafawa da ƙarfafawa mata da jin daɗin yara da kuma kula da ƙungiyoyi masu rauni da sauran al’amuran da ke buƙatar kulawa.
Ta yaba wa NAWOJ reshen jihar Nasarawa bisa jajircewarsu wajen riƙe aikin jaridar da ke da alhaki da ƙarfafawa mata da kuma yaɗa ayyukan cigaba a faɗin jihar.
Hajiya Sule wacce ta samu wakilcin shugabar ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya NUJ reshen jihar Ms. Juliana Ofoku ta buƙaci ‘yan jarida mata da su riƙe ƙa’idojin aikin jarida domin bunƙasa jihar.
Ta bayyana taken taron na “Muna bikinku da gadonmu, muna girmama ƙwarewa, kuma muna ƙarfafa makomar gobe’ a matsayin take mai dacewa da muhimmanci ga cigaban al’umma.
“Wannan take ya dace da lokaci kuma yana karfafawa domin yana tunatar da mu buƙatar kiyaye gadon al’adunmu da kuma girmama mutanen da suka nuna ƙwarewa da hidima. Haka kuma yana kira gare mu mu ƙarfafa sabuwar tsara su ba da gudunmawa wajen cigaban al’ummarmu,” in ji matar gwamnan.
Ta gode wa NAWOJ reshen jihar Nasarawa ɗin bisa karrama ta da lambar yabo bisa gudunmawar da ta bayar ga mata da yara a jihar.
“Wannan karramawa ta ƙara ƙarfafa mini azamar yin hidima da tallafawa da kuma jagorantar ayyukan da za su inganta rayuwa da ƙarfafawa mata a jihar Nasarawa,”- inji ta.
A nata ɓangaren shugabar NAWOJ ta jihar Ms. Mercy Tanze Zabadi ta gode wa gwamnatin jihar da matar gwamna bisa goyon bayan da suke ba wa shirye-shiryen mata.
“A matsayinmu na ‘yan jarida mata mun fahimci babban alhakin da ke kan mu. Mu ne muryar marasa murya muna inganta lissafi da mulki nagari muna kuma kare haƙƙin mata da yara. Haka kuma muna bayyana matsalolin da ke damun al’ummarmu tare da ba da gudunmawa wajen cigaban jihar Nasarawa da Najeriya baki ɗaya,”- inji ta.
Ta buƙaci hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da masu taimakawa su tallafa wa NAWOJ wajen gyara ofishin su da samar da kayan aiki na zamani da faɗaɗa horar da ‘yan ƙungiyar.
Tsohuwar shugabar NAWOJ ta jihar Mrs Veronica Ogbole ta yi jawabi mai taken “Matsayin ‘yan jaridar mata wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya da cigaba mai ɗorewa ” inda ta buƙaci mata ‘yan jarida su kare mutuncin sana’arsu tare da fito da nasarorin mata.
A saƙon fatan alheri ministan harkokin mata Hajiya Imaan Sulaiman Ibrahim wacce Amina Wamba ta wakilce ta, ta buƙaci ‘yan jarida mata da su yi amfani da kafafen yaɗa labarai wajen inganta ilimin ‘yan mata da magance matsalolin da ke cikin al’umma.
Shugabar taron kuma mai bai wa gwamna shawara na musamman Dr Justina Kotso wadda Mrs Tina Cyril ta wakilta ta buƙaci ‘yan jarida matan da su fito da ayyukan cigaba da ba a ba da rahoto ba a kauyuka da kuma ƙara ba da rahoto kan cin zarafin jinsi.
Tsohuwar sakataren damnation jihar hajiya Zainab Ahmed itama ta yaba wa mata masu rike da mukamai bisa nuna ƙwarewa. Ta yi kira ga jam’iyyu da masu ruwa da tsaki da su ba mata dama fiye da haka a zaɓen da ke tafe.
Shugabar NAWOJ ta qasa Ms. Aisha Ibrahim wadda Ms. Chizoba Okonkwo Ogbeche ta wakilce ta ta yaba wa reshen ƙungiyar na Nasarawa bisa ƙaddamar da karrama tsoffin shugabanni da jagororin mata a fagen yaɗa labarai.
A nasa ɓangaren ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Lafia ta tsakiya Hom. Solomon Akwashiki wanda ya ƙaddamar da littafin ya yaba wa shugabancin NAWOJ bisa aikin da suka yi a shekara ta farko. Ya buƙaci ‘yan jarida su kasance masu adalci wajen ba da rahoto.
Mai sharhin littafin wato mallam Shehu Ibrahim mataimakin darakta na yaɗa labarai a ma’aikatar yaɗa labarai na jihar da kuma al’adu da yawon buɗe ido ya bayyana wasu daga cikin waɗanda aka rubuta a littafin kamar Hajiya Amina Wamba a matsayin manyan mutanen tarihi da ya kamata a adana nasarorinsu. Ya bayar da shawarar a rarraba littafin a makarantun firamare da sakandare domin karfafawa ‘yan mata.
Manyan abubuwa da aka gudanar ayayin taron sun hada da ƙaddamar da littafin a hukumance da kuma ba da lambobin yabo ga fitattun mutane da abokan haɗin gwiwa bisa gudummawar da suka bayar ga al’umma musamman jinsin mata.
