Nasarawa: Ma’aikatar noma ta buƙaci Sasakawa Africa ta inganta bincike don wadatar abinci

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Ma’aikatar Noma da Tsaron abinci ta Jihar Nasarawa ta tarbi tawagar Ƙangiyar Sasakawa Africa Association (SAA) yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Lafia babban birnin jihar inda aka tattauna kan yadda za a hanzarta sauya tsarin abinci a jihar da qasa bakidaya.

Dayake jawabi a madadin darakta na SAA a Najeriya Dr. Godwin Atser mai kula da harkokin tsarin noma da kuma wanda ke kula da fannin juriya ga canjin yanayi da Abinci wato Mista Nathaniel Otene sun yi kira ga gwamnati da ta kara zuba jari a fannonin binciken noma da fadakarwa da bada shawarwari ga manoma don inganta harkokin noman nasu a duka matakai.

Otene yace, “Dole ne mu kara karfafa tsarin fadakar da manoma. Idan muka hada shi da fasahar dijital da hadin gwiwa zamu iya rufe gibin da ke tsakanin bincike da amfani da shi a gonaki.”

Ya jaddada mahimmancin saka hannun jari kan matasa tare da tabbatar da cewa duka kanana da manya manoman na samun damar amfani da ayyukan noma na zamani wanda acewarsa zai gina tsarin abinci mai juriya kuma mai daukan kowa.

Darakta Atser ya kuma yo gargadi cewa duk wani sabon bincike da cibiyoyin bincike suka fitar ba zai yi tasiri ba sai an isar da shi yadda ya kamata ga manoman da ke filin.

Ya bayyana cewa SAA a yanzu tana neman hadin gwiwa da gwamnati da cibiyoyin bincike da sauran abokan cigaba dabandaban domin fadada ayyukanta a fadin jihar da qasar nan.

A cewarsa ayyukan SAA a Najeriya na mayar da hankali ne kan mahimman fannonin noma kamar haka:

  1. Noma mai farfado da kasa
  2. Noma dake shafan kasuwanci
  3. Noma mai kula da abinci mai gina jiki
  4. Gina kwarewa da kuma fadakarwa ta zamani da daukar kowa a ciki.

Ya kara da cewa kungiyar na kara karfi wajen yada sabbin nau’in daidaita noma da canjin yanayi da daukar matasa a harkar noma da bunkasa kiwo da sauran su.

A nasu ɓangaren yayin mayar da martanin jawabin, jami’an ma’aikatar noma sun ce za su tabbatar da an karɓi bukatar kuma za a yi la’akari da ita wajen tsara manufofin noma na shekaru masu zuwa.

By Babaji