Kotu ta kori buƙatar EFCC na ƙwace kadarorin Saleh Mamman bayan ya ɗaukaka ƙara

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kotun ƙoli ta Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da wata buƙata da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Tattalin Arziki (EFCC) ta shigar, inda take neman ƙwace wasu kadarori da ake zargin suna da alaƙa da tsohon Ministan Lantarki, Injiniya Saleh Mamman, wanda ya ɗaukaka ƙarar hukuncin da aka yanke masa zuwa Kotun ɗaukaka ƙara.

Mai Shari’a James Omotosho ya soke buƙatar EFCC mai kwanan wata 29 ga Yuli, 2026, wadda aka shigar bisa tanadin Sashe na 20 na Dokar EFCC ta 2004, Sashe na 321 na Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuka ta 2015, da Sashe na 6(6) na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999. An soke buƙatar ne bayan lauyan gwamnati, Abba Mohammed, ya sanar da kotun cewa ya janye ta a hukumance.

Mohammed ya ce, an yanke shawarar janye buƙatar ne bayan Mamman ya ɗaukaka aarar hukuncin gaba ɗaya zuwa Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja.

Buƙatar da EFCC ta shigar tana neman kotu ta bayar da umarnin kwace wa gwamnatin tarayya wasu kadarori da hukumar ta ce ta gano cewa suna da alaƙa da Mamman bayan da aka same shi da laifi kuma aka yanke masa hukunci. Lauyan Mamman, Femi Atteh, bai yi adawa da janye buƙatar ba, yayin da Mai Shari’a Omotosho ya amince da buƙatar tare da soke ƙarar a wani taƙaitaccen hukunci.

A ranar 12 ga Mayu, 2026, Mai Shari’a Omotosho ya same Mamman da laifi kan tuhume-tuhume 12 da suka shafi zargin almundahanar Naira biliyan 33.8, sannan ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 75 a gidan yari, waɗanda za a bi a jere.

Yanzu Mamman ya garzaya Kotun ɗaukaka ƙara ta hanyar sanarwar ɗaukaka ƙara mai kwanan wata 26 ga Mayu, 2026, wadda tawagar lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin Femi Atteh, SAN, ta shigar. Tawagar na neman kotun ta soke hukuncin da aka yanke masa tare da wanke shi daga dukkan tuhume-tuhumen.

ƙarar ta ƙunshi dalilai 18, inda lauyoyin tsohon ministan suka ƙalubalanci wasu matakai da aka bi a lokacin shari’ar da kuma hukuncin da aka yanke masa.

ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka gabatar shi ne zargin cewa an tauye wa Mamman haƙƙinsa na samun shari’a cikin adalci, bayan da aka yanke hukunci a ranar 7 ga Mayu, 2026, ba ya nan, duk da cewa a baya an dage shari’ar zuwa 9 ga Yuni, 2026, domin yanke hukunci.

Lauyansa sun ce an sauya ranar yanke hukuncin ba tare da an sanar da shi ba, kuma bai taɓa yin watsi da haƙƙinsa na halartar zaman kotu ba. A cewarsu, hakan ya saɓa wa Sashe na 36 na Kundin Tsarin Mulkin 1999 da Sashe na 352(4) na Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuka ta 2015.

Sauran dalilan ɗaukaka ƙarar sun haɗa da zargin cewa alkalin shari’ar ya hana wani shaidan da Mamman ya nema ta hanyar umarnin kotu, Abdulkareem Ozi Ibrahim, bayar da shaida a madadinsa. Ibrahim ya kasance Daraktan Asusun Ayyuka na Musamman a Ofishin Akanta-Janar na Tarayya.

Lauyoyin tsaron sun kuma ce an ba masu gabatar da ƙara damar sake fara yi wa wannan shaidan tambayoyi na farko, bayan da suka rufe gabatar da shari’arsu kuma aka dage zaman domin yi masa tambayoyin giciye.

ƙari kan haka, masu kare Mamman sun ce hukuncin ya dogara sosai kan shaidar wani abokin aikata laifi da ba a samu wata shaida mai zaman kanta da ta tabbatar da ita ba, sannan kuma sun yi zargin cewa an yanke hukunci kan tuhume-tuhume na 7 zuwa 12 ba tare da an karɓi iƙirarin Mamman kan waɗannan tuhume-tuhumen ba.

Wani dalilin ɗaukaka ƙarar ya shafi hukuncin kotun cewa an karkatar da kuɗaɗen ayyukan samar da wutar lantarki na Zungeru da Mambilla domin amfanin Mamman. Lauyansa sun ce kuɗaɗen suna ƙarƙashin Babban Bankin Nijeriya (CBN), yayin da Ofishin Akanta-Janar na Tarayya ke kula da su, kuma Mamman ba shi ne jami’in da ke da ikon amincewa da kuɗaɗen ko kuma wanda ke da damar sanya hannu kan asusun ba.

Tawagar lauyoyin Mamman ta kuma ce wasu muhimman abubuwan da kotun ta dogara da su sun samo asali ne daga jita-jita, tare da yin watsi da wasu takardun shaida, abin da suka ce ya kai ga yin hasashe.

Sun ƙara da cewa kotun ta ɗora wa Mamman nauyin tabbatar da rashin laifi, bayan da ta ce ya kasa bayyana tushen kuɗin da aka yi amfani da su wajen sayen wata kadara da ke lamba 12 a titin Lungi da ke yankin Wuse II a Abuja.

ƙarar ta kuma ƙalubalanci yadda aka karɓi wasu bayanan Mamman da ya bayar a wajen kotu, inda lauyansa suka ce an karɓe su ba tare da bin tanadin Sashe na 15 da 17 na Dokar Gudanar da Shari’ar Laifuka ta 2015 ba, ciki har da rashin adana bayanan ta hanyar sauti da bidiyo. Lauyoyin sun kuma zargi alƙalin shari’ar da nuna son kai a fili a kansa a tsawon lokacin shari’ar, lamarin da suka ce ya haifar da rashin adalci.

By ukarofi

Leave a Reply