Zamfara: A Oktoba za a fara jigilar fasinjoji daga Gusau zuwa Abuja a sabon filin jiragen saman jihar – Gwamnati

Spread the love

Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa da kamfanin XEJet Limited domin fara zirga-zirgar jiragen fasinja kai tsaye tsakanin Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau da Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Yarjejeniyar Fahimtar Juna, wato MoU da aka sanya wa hannu ranar Litinin ta zama wani muhimmin mataki wajen inganta zirga-zirgar jama’a da kuma sauƙaƙa harkokin kasuwanci, zuba jari, yawon buɗe ido da bunƙasar tattalin arzikin Jihar Zamfara.

Wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa Mataimakin Gwamnan jihar, Malam Mani Mummuni, ne ya jagoranci bikin sanya hannu kan yarjejeniyar. Sanarwar ta ƙara da cewa, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Mohammed Nakwada, ne ya sanya hannu a madadin gwamnatin jihar.

Sanarwar ta ce, “Gwamnatin Jihar Zamfara ta sanya hannu kan Yarjejeniyar Fahimtar Juna (MoU) da kamfanin XEJet Limited kan bunƙasa hanyar zirga-zirgar jiragen sama, domin fara zirga-zirgar jiragen fasinja tsakanin Abuja da Gusau. “Ƙarƙashin yarjejeniyar, XEJet zai fara zirga-zirgar jirage sau biyu a kowane mako daga wata mai zuwa.

“Sabuwar hanyar zirga-zirgar jiragen sama za ta inganta damar zuwa Zamfara tare da buɗe ƙarin damammaki ga masu zuba jari, ’yan kasuwa da baƙi.”

Da yake jawabi a wajen bikin, Mataimakin Gwamna Mani Mummuni ya ce haɗin gwiwar ya yi daidai da manufar gwamnatin jihar ta inganta ababen more rayuwa na sufuri. Ya ce, “An gina Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau ne tun daga tushe, kuma aka kammala shi cikin shekaru biyu. Babbar manufar gina filin jirgin shi ne sauƙaƙa tare da inganta zirga-zirgar mutane da kayayyaki, abin da zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.”

“Gwamna Lawal yana ci gaba da neman masu zuba jari na ƙasa da ƙasa da hukumomin bayar da tallafi, waɗanda dukkansu suke da niyyar zuba jari a Zamfara,” inji shi.

A ƙarshe, ya ce “Wannan matakin fara zirga-zirgar jiragen kasuwanci zai jawo hankalin masu zuba jari. Inganta damar isa jihar ita ce babbar manufarmu, domin hakan zai samar da yanayi mai kyau ga bunƙasar kasuwanci da zuba jari.”

By Babaji

Leave a Reply