
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kano ta ce ta kama wani ɗan shekara 35 da ake zargin mai garkuwa da mutane kuma ɓarawon dabbobi ne mai suna Habibu Bello, a yayin wani atisaye a yankin iyakar Kano da Kaduna.
Rahotanni sun bayyana cewa, Bello, wanda ɗan garin Kunkumi ne na Ƙaramar Hukumar Maƙarfi ta Jihar Kaduna, an kama shi ne a ranar 14 ga Satumba bayan samun wasu bayanan sirri daga tawagar yaƙi da garkuwa ta rundunar.
Kakakin ‘yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya sanar da haka a wata takarda, inda ya ce ana zargin mutumin mamba ne na wata daba da take da hannu a garkuwa, fashi da makami da kuma satar dabbobi a sassan jihohin, Kano, Kaduna da Katsina. Ya ce, a sakamakon faɗaɗa bincike, an kuma kama wani ɗan dabar mai suna Mudam na Kwanar Ɗangora.
A cewar ‘yan sanda, ana zargin Bello da hannun a ayyukan garkuwa da dama, ciki har da sace wata Hajiya Binta ‘yar Kwanar Ɗangora, inda aka yi zargin sai da aka biya Naira miliyan 20 a matsayin kuɗin fansa kana aka sako ta. CSP Kiyawa ya ƙara da cewa, ana cigaba da gudanar da bincike domin kamo sauran mambobin dabar da ƙwato makamansu.
A wani atisayen kuma, rundunar ta ce ta gano wata na’urar leƙen asiri (Cine-Camera Drone marked GT 50) a yankin ƙauyen Hawan Tarau da ke Ƙaramar Hukumar Bebeji a jihar a ranar 17 ga Satumba. Ta ce, an tsinci na’urar ne yashe a ƙasa, inda kuma ana bincike don gano haƙiƙanin tushenta.
Kwamishinan ‘yan sandan, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yi kira ga mazauna da su riƙa ruwaito dukkan wani abin zargi da suka gani a yankunansu ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su ko kuma ta lambobinta na bayar da agajin gaggawa kamar haka: 08032419754, 08123821575 da kuma 09029292926.
