Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta bayyana cewa tsawaita zaman Ibrahim Magu a matsayin Muƙaddashin Shugaban Hukumar Yaƙi da Yiwa Tattalin Arziƙi Zagon ƙasa (EFCC) ya saɓa wa doka, inda ta soke wani hukuncin Babbar Kotun Tarayya da a baya ya amince da ci gaba da riƙe shi a matsayin mukaddashin shugaban hukumar.
Kwamitin alkalai uku na Kotun ɗaukaka ƙarar ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, bayan sauraron ƙarar da wani lauya, Johnmary Jideobi, ya shigar kan ci gaba da zaman Magu a matsayin mukaddashin shugaban EFCC, bayan da Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da naɗinsa a matsayin cikakken shugaban hukumar sau biyu.
ƙarar ta samo asali ne daga hukuncin da Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke a ranar 4 ga Disamba, 2019, inda ta yi watsi da ƙarar da aka shigar domin ƙalubalantar ci gaba da zaman Magu a matsayin mukaddashin shugaban hukumar.
Magu ya kasance mukaddashin shugaban EFCC daga shekarar 2015 zuwa watan Yulin 2020, lokacin da aka dakatar da shi daga aiki.
Jideobi ya shigar da ƙarar farko a Babbar Kotun Tarayya a watan Maris na shekarar 2017, yana mai cewa Magu ba zai iya ci gaba da kasancewa a matsayin mukaddashin shugaban hukumar ba har abada bayan da Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da naɗinsa.
A hukuncin da ta yanke a shekarar 2019, Mai Shari’a Ojukwu ta ce Dokar Kafa EFCC, musamman sashe na 2(3), ba ta takaita ikon Shugaban ƙasa na ci gaba da riƙe Magu a matsayin mukaddashin shugaban hukumar ba.
Alƙalin ta bayyana cewa akwai gibi a cikin dokar, domin ba a fayyace takamaiman lokacin da mutum zai iya ɗauka yana aiki a matsayin mukaddashin shugaban EFCC ba. Saboda haka, ta ce wannan gibi ya bai wa Shugaban ƙasa damar ci gaba da riƙe mukaddashin shugaban hukumar.
Ta kuma bayyana cewa Order 1(2)1 na Dokokin Majalisar Dattawa da mai ƙarar ya dogara da shi ya shafi naɗa ministoci ne kawai, kuma ba za a iya amfani da shi wajen matsayin mukaddashin shugaban EFCC ba.
Haka kuma, Mai Shari’a Ojukwu ta ce Jideobi ba shi da isasshen matsayi na shari’a (locus standi) da zai ba shi damar shigar da ƙarar.
Sai dai Jideobi bai gamsu da hukuncin ba, inda ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun ɗaukaka ƙara. Ya yi zargin cewa shugaban EFCC yana da wa’adin shekaru huɗu ne, wanda za a iya sabunta shi sau ɗaya, kuma Magu ya zarce lokacin da doka ta tanada ba tare da samun amincewar Majalisar Dattawa ba.
Ya kuma yi hujjar cewa naɗin Magu na riƙon ƙwarya ya ƙare ne bisa tanadin doka bayan Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da naɗinsa a matsayin cikakken shugaban hukumar.
Jideobi ya nemi Kotun ɗaukaka ƙara da ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya tare da amincewa da buƙatun da ya gabatar a ƙarar tasa ta farko.
Wadanda aka sanya a matsayin waɗanda ake ƙara a shari’ar sun haɗa da Majalisar Dattawa, Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Hukumar EFCC da Ibrahim Magu.
Magu ya bar matsayin mukaddashin shugaban EFCC a watan Yulin 2020, bayan tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya dakatar da shi. Daga baya, Mohammed Umar Abba, wanda a lokacin shi ne Daraktan Ayyuka na EFCC, ya karɓi matsayin mukaddashin shugaban hukumar.
Daga baya, an naɗa Abdulrasheed Bawa a matsayin cikakken shugaban EFCC a watan Fabrairun 2021, kafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shi a watan Yunin 2023. Daga bisani aka naɗa Ola Olukoyede a matsayin shugaban EFCC na yanzu.
Hukuncin na Kotun ɗaukaka ƙara ya sauya matsayin shari’a da Babbar Kotun Tarayya ta ɗauka a shekarar 2019 kan halaccin tsawaita zaman Magu a matsayin mukaddashin shugaban EFCC.
