Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da biyan Naira biliyan 3.659 ga ’yan fansho, ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya da kuma iyalan ma’aikatan da suka rasu, inda mutane 1,339 da ke ƙarƙashin tsarin Contributory Pension Scheme (CPS) da Defined Benefit Scheme (DBS) za su amfana.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Al’adu na jihar, Malam Ahmed Maiyaki, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce sabon biyan ya kawo jimillar kuɗaɗen fanshon da gwamnatin Uba Sani ta biya tun bayan hawanta mulki a watan Mayun 2023 zuwa Naira biliyan 21.455, waɗanda mutane 9,683 suka amfana.
A cewar kwamishinan, daga cikin waɗanda za su amfana da sabon biyan, ’yan fansho 210 na ƙananan hukumomi za su karɓi Naira miliyan 515 ƙarƙashin tsarin DBS.
Ya ƙara da cewa Naira biliyan 3.144 za a raba wa mutane 1,129 ƙarƙashin tsarin CPS, waɗanda suka haɗa da ’yan fansho 402 na ma’aikatan jihar da kuma 727 na ƙananan hukumomi.
Malam Maiyaki ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar na magance basussukan fansho da inganta tsarin biyan hakkokin ma’aikatan da suka yi ritaya.
Ya ce gwamnatin na kuma aiwatar da wasu sauye-sauye a harkokin kuɗaɗen gwamnati domin tabbatar da gaskiya, riƙon amana da dorewar tsarin fansho a jihar.
Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani ya yi imanin cewa biyan fansho ba alfarma ba ce, illa wajibi ne ga mutanen da suka sadaukar da shekarun rayuwarsu wajen yi wa jihar hidima.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin za ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyaren tsarin fansho tare da ƙoƙarin rage sauran basussukan da ake bin gwamnati, domin bai wa ma’aikata damar yin ritaya cikin mutunci da kwanciyar hankali.
