Kishi tsakanin ma’aurata: Zargi ko ƙauna da ke barazana ga zaman aure

Spread the love

Daga DR. BILKISU YUSUF ALI 

Gabatarwa:

Aure wata alaƙa ce da aka gina bisa soyayya, amana, mutunta juna, haƙuri da fahimtar juna. Ma’aurata suna buƙatar su ji cewa suna da matsayi na musamman a wajen junansu. A cikin wannan yanayi ne kishi yake iya bayyana. Kishi ba sabon abu ba ne a tsakanin ma’aurata, a wasu lokuta yana iya kasancewa wata alama ce ta damuwa ko tsoron rasa wanda mutum yake ƙauna. Amma idan kishi ya wuce iyaka, ko ya wuce gona da iri, abin da aka fara da shi a matsayin ƙauna na iya rikiɗewa ya zama matsala mai girma a cikin gida. Kishi na iya farawa ne da tambaya kamar: “Ina ka je?”, “Wa ka ke magana da ita?”, ko “Me ya sa ki ka daɗe ki na waya?” Idan aka samu fahimtar juna, irin waɗannan tambayoyi na iya zama na yau da kullum. Amma idan suka koma bincike marar ƙarewa, zargi, leƙen waya, hana abokai, hana zuwa wuraren da suka dace ko kuma yawan tuhuma ba tare da hujja ba, hakan na iya jefa aure cikin matsala.

Akwai bambanci tsakanin kishi da rashin yarda. Kishi mai matsakaici na iya kasancewa cikin dangantaka, amma rashin yarda mai tsanani na iya sa mutum ya riƙa ganin kuskure a duk abin da abokin zamansa yake yi. Wannan shi ne dalilin da ya sa ya kamata ma’aurata su fahimci inda kishi yake ƙarewa, da kuma inda yake fara wa a zaman aure kafin ya zama barazana ga zaman lafiyar iyali.

Me ke jawo kishi tsakanin ma’aurata?

Dalilan kishi ba ɗaya ba ne, don haka dalilan da suke janyo kishi suna da yawa. Wasu suna da alaƙa da abubuwan da suka faru a baya, wasu kuma suna da alaƙa da yadda mutum yake kallon kansa ko yadda yake fahimtar aure ko mu’amala da kuma tariyar rayuwar baya,

1. Rashin amincewa:

Rashin amincewa na daga cikin manyan abubuwan da ke ƙara kishi. Idan mutum bai yarda da abokin aurensa ba, ko da kuma abin da yake yi, to da matsala, zai iya fassara shi ta hanyar da ba daidai ba. Misali, idan miji ya ga matarsa tana magana da wani mutum cikin girmamawa wanda bai sani ba, zai iya ɗauka cewa akwai wata alaƙa ta daban. Haka nan, mace na iya ganin mijinta yana magana da wata mace a wurin aiki, ta fara tunanin cewa akwai wani abu a tsakaninsu. A irin wannan yanayi, matsalar ba wai abin da aka gani kawai ba ce; matsalar ita ce yadda aka fassara abin.

2. Abubuwan da suka faru a baya:

Wasu mutane sun taɓa fuskantar cin amana ko ƙarya a wata dangantaka da ta gabata. Saboda haka, idan suka yi aure suna iya ɗaukar tsoron abin da ya faru a baya zuwa sabon gidan.

Mutumin da aka taɓa yaudara na iya samun wahalar sake amincewa. Amma ya kamata a fahimci cewa sabon abokin aure ba lallai ne ya zama kamar wanda ya cutar da mutum a baya ba.

3. Rashin sadarwa:

Idan ma’aurata ba sa magana cikin gaskiya da natsuwa, ƙananan abubuwa na iya zama manyan matsaloli. Miji ya fita bai faɗa wa matarsa inda zai je ba. Matar ta kira shi, bai ɗaga waya ba. Sai ta fara tunani. Shi kuma ya dawo gida ya ga tana fushi, sai ya ɗauka tana son ta takura masa. Haka matsala ke girma daga ƙaramin abu. Sadarwa mai kyau tana taimakawa wajen rage zato.

4. Tasirin wasu mutane:

Wasu lokuta kishi ba daga cikin ma’auratan yake farawa ba. Aboki, ƙawaye, ’yan uwa ko ma wasu masu son kawo fitina na iya faɗin magana kamar:

“Na ga mijinki yana yawan magana da waccan matar.”

“Ki kula da shi, maza ba a yarda da su.”

“Me ya sa matarka take yawan fita?”

Idan mutum bai yi bincike ba, irin wannan magana na iya zama tushen matsala a aure.

5. Social media da wayoyin zamani:

A zamanin yau, wayar hannu ta zama wani ɓangare na rayuwar mutane. Ma’aurata suna amfani da WhatsApp, Facebook, TikTok, Instagram da sauran hanyoyin sadarwa. Wasu lokuta mutum yana ganin hoton abokin aurensa da wani, ko ya ga saƙo daga wata mace ko wani namiji, sai a fara zargi. Amma abin da aka gani a social media ba koyaushe yake nuna cikakken gaskiyar abin da ke faruwa ba. Saboda haka, yanke hukunci cikin gaggawa na iya haifar da rikici.

Yadda kishi yake bayyana a cikin aure:

Kishi yana iya bayyana ta hanyoyi daban-daban.Wasu suna yawan tambayoyi. Wasu suna yin shiru su ɓoye fushinsu. Wasu kuma suna nuna fushi kai tsaye. A wasu gidaje, mutum zai iya fara son sanin duk wanda abokin aurensa yake magana da shi, inda yake, lokacin da zai dawo da kuma dalilin da ya sa ya yi wani abu. A wasu lokuta kuma kishi yana iya kaiwa ga yawan zargin cin amana ba tare da hujja ba. Wata matsala ita ce mutum na iya fara ɗaukar kishi a matsayin hujjar soyayya. Yana cewa: “Ina kishinki, saboda ina sonki ne.”Gaskiya ne cewa mutum na iya yin kishi saboda yana ƙauna, amma soyayya ba ta ba mutum izinin tauye mutuncin abokin aurensa ba. Soyayya tana buƙatar amana, yayin da kishi mai tsanani yake iya lalata wannan amana.

Illar kishi ga zaman aure:

Kishi idan ya wuce iyaka yana iya haifar da matsaloli masu yawa kamar haka:

Rashin kwanciyar hankali

Gida ya kamata ya kasance wurin samun nutsuwa. Idan kowane abu yana zama dalilin zargi, gida zai iya zama wurin tashin hankali da damuwa. Miji yana iya jin cewa duk abin da ya yi za a tambaye shi. Mace ma tana iya jin cewa ba a yarda da ita ko ba a fahimce ta.

Lalacewar amana

Aure yana buƙatar amana. Idan mutum kullum yana zargin abokin aurensa, hakan na iya sa wanda ake zargin ya ji cewa ba a daraja shi. Idan aka rasa amana, abubuwa da yawa suna fara lalacewa.

Nisantar juna

Wasu ma’aurata da kishi ya yi musu yawa suna fara rage magana da juna. Maimakon su zauna su tattauna matsala, sai kowa ya fara rayuwa shi kaɗai.Wannan na iya haifar da ƙarin rashin fahimta.

Shafar tarbiyyar yara

Idan yara suna ganin iyayensu kullum suna rigima saboda kishi, hakan na iya shafar yadda suke kallon aure da dangantakar iyali. Yaro yana iya fara ganin cewa aure kullum rigima ne, ko kuma ya ɗauki halayen da yake gani a gida ya kai su rayuwarsa ta gaba.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa insha Allah.

By ukarofi

Leave a Reply