Legas ta yi fintinkau yayin da INEC ta fitar da jerin rijistar masu zaɓe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Yayin da ake cigaba da tunkarar babban zaɓen 2027, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta fitar bayyana jihohi masu mafiya yawan adadin rajistar masu zaɓe, inda Legas Kano da Kaduna suke kan gaba. Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ne ya bayyana adadin a ranar Talata a Abuja a lokacin da yake jawabi kan shirye-shiryen hukumar ga zaɓukan na 2027 da ke cigaba da ƙaratowa.

A cewarsa, Legas ce take jagorantar jaddawalin da jimillar rajistar masu zaɓe guda 7,488,633, sai Kano mai 6,570,276 da kuma Kaduna mai guda 4,662,640. Katsina ita ce jiha ta huɗu da masu rajistar zaɓe 3,876,051, yayin da Ribas ta zo ta biyar da mutum 3,736,434. A mataki na shida akwai Oyo mai guda 3,588,111 sai Delta da 3,525,988.

Jihar Benuwai ce ta takwas mutum 3,057,225, yayin da Ogun take da 3,037,981 da Bauchi a mataki na goma da rajista 3,012,547. Amupitan ya ce Abuja tana da 1,732,043 a mataki na mafi ƙarancin rajista na uku.

Ya ƙara da cewa, Ekiti ce mai mafi ƙaranci rajista, wadda take da 1,055,708, sai Bayelsa mai 1,200,691 da guda 1,733,641 ga Yobe. Gombe kuma tana da 1,768,566.

Sannan farfesan ya ce, akwai maza guda 53,528,218, wanda ke wakiltar kaso 51.75 na masu rajistar, yayin da 49,900,497 shi ne adadin mata. Amupitan ya ce wannan ɓangare ne na aikin hukumar na bayar da ba’asin adadin rajistar masu zaɓe a jihohin Nijeriya gabanin zaɓen 2027.

Ya bayyana cewa, an samu gagarumar nasara a harkokin rajistar masu zaɓe a Nijeriya bayan kammala zango uku na yi wa al’umma rajista da kuma tsarin ƙarshe na na’ura, wanda hakan ya taimaka wajen samun ƙarin wasu mutum miliyan 10.7 a matsayin sababbin masu rajista har zuwa lokacin da na’urar ABIS za ta tantance su.

Saidai a wani jawabi a taron, Shugaban na INEC ya ce jimillar adadin masu zaɓe ya kai miliyan 110, wanda ya nuna akwai saɓani kan ainihin adadin saboda shafin yanar gizo na INEC ya nuna wani adadi daban, don haka adadin na jihohin da aka zayyano, sune waɗanda farfesan ya sanar.

Haka kuma, INEC ta sanar da cewa za ta fara aikin bayarwa da karɓar katin zaɓe (PVC) a ranar Juma’a, 9 ga Oktoba, 2026. Amupitan ya bayyana cewa hukumar ta riga ta kammala aiki da miƙa wa ƙananan hukumomi ɗibar farko na katinan zaɓe gabanin fara rabawa.

A ranar 16 ga Junairu ne dai za a gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa da na Majalisar Dokokin Ƙasa, yayin da za a yi na gwamnonin da majalisun dokokin jihohi a ranar 6 ga Fabarairu, 2027, kamar yadda INEC ta bayyana a jaddawalin ayyukanta.

By Babaji

Leave a Reply