Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Zamfara kuma jakadan zaman lafiya a Afirka, Hon. Sani Gwamna Mayanchi, ya nuna damuwa kan yadda rashin tsaro ya addabi Zamfara, yankin Arewa maso Yamma da wasu sassan ƙasar nan.
Hon. Mayanchi ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya gudanar a Gusau yau Laraba.
Ya ce zargin da ake yi na rashin bai wa mambobin jam’iyyar APC kuɗaɗe da tallafi ba shi da ma’ana, kuma zai iya jawo rashin fahimta da kuma ɓata sunan gwamnatin jihar.
Ya ce ya kamata mambobin APC su ba gwamnatin jihar shawara kan matsalar rashin tsaro da ta addabi wasu al’ummomi, maimakon su riƙa neman a basu kuɗaɗe ko wani tallafi domin buƙatar kansu.
Ya soki masu ƙalubalantar gwamnatin jihar kan rashin basu kuɗi ko tallafi, inda ya ce, gwamnatin jihar, ƙaramin ministan tsaro, Dr. Bello Matawalle, Sanata Abdulaziz Yari da sauran manyan ‘yan siyasa suna tare da jama’a ta fuskar rabaon tallafi a ko yaushe.
Ya tabbatar da cewa Jihar Zamfara na daga cikin jihohin da ke bayar da tallafi, musamman ta fuskar gina ababen more rayuwa da suka shafi rayuwar al’ummar jihar kai tsaye.
“Nayi tsammanin mambobin APC za su ba gwamnatin jiha da ta tarayya shawara kan matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar mu a yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a gidan gwamnati kwanan nan, amma abin takaici sun saka buƙatun kansu a gaba, wannan ba dimokuraɗiyya ba ne kuma abin da bai dace ba ne,” in ji shi.
Ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta tarayya da su ƙara ƙoƙari wajen magance matsalar rashin tsaro a jihar, yankin Arewa maso Yamma da ƙasa baki ɗaya.
Hon. Mayanchi ya yi kira da a samu haɗin kai a tsakanin mambobin APC a jihar, yana mai jaddada cewa rarrabuwar kai da son kai na iya haifar da rikici wanda zai iya janyo faɗuwar jam’iyyar a zaɓe mai zuwa.
“Ina kira ga dukkan mambobi da magoya bayan APC da su ci gaba da kasancewa tare da tabbatar da nasarar jam’iyyar maimakon su riƙa yaɗa ƙaryar bayanan da ka iya haifar da rarrabuwar kai a cikinsu,” in ji shi.
A cewarsa, APC abu ɗaya ce a Zamfara, yana mai jaddada cewa za su cigaba da neman goyon baya don samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dauda Lawal a zaɓe mai zuwa.
