AKCOE ta yaye ɗaliban da suka kammala digiri a karo na farko — Dakta Ayuba

Spread the love

Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano

A karon farko, Kwalejin Ilimi ta Aminu Kano, wadda aka fi sani da AKCOE, ƙarƙashin jagorancin Dr. Ayuba Ahmad Muhammad, mai haɗin gwiwa da Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA), ta gudanar da bikin yaye ɗalibai maza da mata da suka kammala karatunsu na digiri a fannoni daban-daban.

Shugaban kwalejin ya bayyana hakan ne a wani gagarumin biki da aka gudanar a ƙarshen makon da ya gabata a birnin Kano.

Haka kuma, ya ƙara da cewa wannan kwaleji na daf da zama jami’a, kamar yadda shugaban kwalejin ya bayyana a lokacin bikin yaye ɗaliban da suka kammala digirinsu na farko a wannan kwaleji mai haɗin gwiwa da FUDMA.

Dakta Ayuba AM ya ƙara da cewa tun farko an kafa wannan kwaleji ne domin tallafa wa ɗaliban da suka kammala sakandare domin su samu damar yin karatun NCE, wato takardar shaidar koyarwa ta ƙasa, da kuma Diploma a fannoni daban-daban, da sauran karatun da zai taimaka wa waɗanda suka kammala sakandare wajen samun damar ci gaba da zurfafa karatu.

Ya ce hakan ya yi daidai da manufofin Gwamnatin Jihar Kano, Gwamnatin Tarayya da sauran masu kishin ilimi.

A sakamakon wannan ci gaba, kwalejin AKCOE ta haɗa kai da FUDMA domin ba matasa damar yin karatun digiri da digirgir. Ya ce abin godiya ne ga Allah ganin yadda wasu ɗalibai suka samu damar kammala digiri a wannan kwaleji.

Ya yabawa hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a harkar bunƙasa ilimi bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaban ilimi a Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa kashi 90 cikin 100 na waɗanda suka kammala wannan makaranta sun yi karatunsu ta hanyar amfani da wayar hannu, inda ya ce wannan tsari ya bai wa ɗalibai damar yin karatu cikin sauƙi.

Ya ce da wannan karatu, ɗalibi zai iya shiga jami’a da zarar ya cika sharuɗɗan shiga jami’a a Nijeriya.

Ya kuma bayyana cewa makarantar tana da tsarin ci gaba da karatu tare da wasu jami’o’i, ciki har da Jami’ar Muhibu da wata jami’a da ke ƙasar Kenya da sauran cibiyoyin ilimi.

A ƙarshe, Dakta Ayuba ya bayyana cewa da zarar wannan kwaleji ta zama jami’a, ɗalibai ’yan asalin Jihar Kano 1,000 za su samu damar yin digiri kyauta a wannan jami’a.

Ya kuma bayyana cewa a yanzu haka Gwamnatocin Jihohin Nasarawa, Neja da Kaduna da sauransu na neman haɗin gwiwar AKCOE domin bunƙasa ilimi bisa tsarin da wannan kwaleji take amfani da shi a birnin Kano.

By ukarofi

Leave a Reply