Sojoji sun fara farautar baƙin akwatin jirgin da ya yi hatsari a Ondo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar Sojin Saman Nijeriya (NAF) ta ce ta fara ƙoƙarin gano baƙin akwati da na’urar ɗaukar murya jirgin ATR-42 da ya yi hatsari a Igbokoda da ke Ƙaramar Hukumar Ilaje ta Jihar Ondo a makon day a gabata. Jami’i SSE Ebimobo Ebiowe, wanda mataimakin air vice marshal ne ya bayyana haka ga ‘yan jarida a wajen da hatsarin ya faru a ranar Juma’a.

Al’amarin ya auku ne a lokacin da jami’an NAF suka taso daga Benin City na jihar Edo suka nufi Legas, a kusa da sansanin FOB na NAF a ranar Litinin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar baki ɗaya mutane 25 da ke cikin sa.

Jami’ai sun ce jirgin ya rabe ne gida biyu a lokacin da yake faɗowa, inda gangan jikinsa ya rabu da injinsa daga nisan mita 30 daga sararin samaniya. Wannan al’amari ya sa gano gawarwaki da sassan jirgin ya yi wahala. Haka kuma, sai da gwamnatin jihar Ondo ta ɗauki tsawon sa’o’i 48 kafin tura kayan aikin bincike domin aiwatar da aikin yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa, jami’an soji da jama’ar gari sun cigaba da ɗebo sassan ɗan-adam da na jirgin, amma ba su iya samo ainihin kwanson jirgin ba Sannan, masu aikin ceto sun ce sassan jikin mamatan sun gurɓata ruwan, yayin da zubar man jirgin ya haifar da wari mai tsananin a yankin ruwan. A cewar Ebiowe, masu bincike na cigaba da ƙoƙarin nemo bayanai domin gano ainihin yadda al’amarin ya auku.

Kazalika, ya ce baƙin akwatin da ke kira da Flight Data Recorder da na’urar ɗaukar murya, Cockpit Voice Recorder sune muhimman ababen da masu bincike suke ƙoƙarin ganowa.

By Babaji

Leave a Reply