Duk da cire tallafin fetur ya haifar da matsi, gwamnatinmu ta samar da tiriliyan N3.3 daga ragin harajin fetur, inji Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa yana sane da matakin gwamnatinsa na cire tallafin fetur ya haifar da matsi ga magidanta da dama a Nijeriya, inda ya ce gwamnatin tana ƙoƙarin samar da hanyoyin rage ƙarfin tasirin hakan. Tinubu ya ce, wannan mataki ya zo ne tare da nauyin samar da mafita domin rage tsadar sufuri, musamman ga ‘yan Nijeriya da suke fafutukar samun sauƙin lamuran sufuri.

Shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a wani saƙon da aka wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi, inda yake bayar da misali da motocin bos masu amfani da lantarki da masu amfani da hasken rana a matsayin shirin samar da sauƙin farashin sufuri a jihohin Nijeriya da dama.

Ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya tana aiki da na jihohi ta hannun ƙungiyar gwamnonin Nijeriya da masu zuba jari masu zaman kansu domin faɗaɗa hidimar Shirin Samar da Sauƙin Sufuri ta CNG na Ƙasa. A cewarsa, a kwanan nan ne Jihar Ekiti ta karɓi motocin bos guda 15, Legas 20, Akwa-Ibom tana da guda 50 da suka shirya fara aiki.

Ya ƙara da cewa, Jihar Katsina ta samar da bos 30 na CNG da adaidaita sahu masu amfani da lantarki 200, yayin da Kano ta samu bos ɗin CNG 30 da masu amfani da lantarki biyar. Kuma ana shirin kafa tsarin a Jihar Edo nan ba da jimawa ba. Sannan, shugaban ya ce bos ɗin CNG 100 na Jihar Kaduna sun yi zirga-zirga da mutane aƙalla sama da miliyan uku zuwa yanzu.

Kazalika, Shugaba Tinubu ya ce yana sane da halin matsin da al’umma suka shiga a sanadiyyar hauhawar farashin fetur musamman ga magidanta da ‘yan kasuwa, inda ya ce gwamnatin ta yafe haraji da kuɗaɗen ƙa’idar fetur na sama da Naira tiriliyan 3.3 a matsayin matakin rage tasirin hauhawar farashin kayayyaki akan ‘yan Nijeriya. Ya ce, NNPCL zai yafe wani kaso na ribar da yake samu na tsawon kwanaki 30 musamman domin masu harkar sufuri na ‘yan kasuwa, yayin da gwamnatin kuma take aikin samar da sauƙin farashin litar fetur a ƙasar domin rage wa al’umma raɗaɗin halin da suke ciki.

By Babaji

Leave a Reply