Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta gargaɗi masu sana’ar POS da su guji karɓar kuɗi daga majiyoyin da ba a san asalinsu ba, tare da amfani da asusun bankunansu wajen karɓa ko tura kuɗin da ba su tantance sahihancinsa ba.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DSP Aliyu Abubakar Sadiq, ne ya bayyana hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan kuɗaɗe na iya kasancewa kuɗin da aka samu ta hanyar aikata laifuka, wanda zai iya jefa masu POS cikin matsalar binciken jami’an tsaro da kuma fuskantar hukunci a gaban doka, ko da ba su san asalin kuɗin ba.
Ya buƙaci masu POS da su riƙa tantance mutanen da suke hulɗa da su da kuma sahihancin kowace mu’amalar kuɗi kafin su karɓa ko su miƙa kuɗin.
DSP Aliyu Abubakar Sadiq ya jaddada cewa kare kai daga matsalar shari’a ya fi son zuciya saboda kuɗin cajin POS, yana mai kira ga masu sana’ar da su gudanar da harkokinsu cikin gaskiya da bin ƙa’ida.
