Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya buƙaci waɗanda suka amfana da tallafin abinci ƙarƙashin shirin Renewed Hope Initiative da su yi amfani da kayan abincin wajen ciyar da iyalansu, maimakon sayar da su.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin rabon tallafin abincin da Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ƙaddamar a gidan gwamnatin Katsina, inda jihar ta zama ta 30 da ta amfana da shirin.
A yayin taron, Raɗɗa ya bayyana wasu nasarorin da gwamnatinsa ta samu a ƙarƙashin shirin Building Your Future Agenda, waɗanda suka haɗa da gina sabbin makarantun sakandare 170, ɗaukar malamai sama da 10,000 aiki, samar da taraktoci sama da 400 da farfaɗo da cibiyoyin kiwon lafiya sama da 200.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta ɗauki ma’aikatan sa-kai na tsaron al’umma sama da 3,000 aiki tare da sayo motocin sulke sama da 20 domin ƙarfafa tsaro.
A nata jawabin, Sanata Oluremi Tinubu wadda uwargidan mataimakin shugaban ƙasa ta wakilta ta buƙaci gwamnonin jihohi su kafa bankunan abinci a yankunan sanatoci uku na kowace jiha, domin yaƙi da ƙarancin abinci da matsalar rashin gina jiki, musamman ga yara da mata masu juna biyu da masu shayarwa.
Ita kuwa Uwargidan Gwamnan Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Raɗɗa, ta bayyana cewa an raba sama da naira miliyan 125 ga tsofaffi 750 cikin shekaru uku, baya ga tallafin da ake bai wa mata masu sana’o’i da ƙananan ’yan kasuwa.
