Yadda aka sace mahaifiyata bayan na fallasa badaƙalar Dala 2.4bn na tallafi a 2012 – Okonjo-Iweala

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Darakta-Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Dakta Ngozi Okonjo-Iweala da tunatar da yadda aka yi garkuwa da mahaifiyarta a Disambar 2012 bayan ta bankaɗo wani zargin badaƙalar kuɗaɗen tallafin fetur da adadinsu ya kai Dala biliyan 2.4 a lokacin da take riƙe da muƙamin Ministar Kuɗin Nijeriya.

Ngozi Okonjo-Iweala ta ce bincike akan zargin badaƙalar ya kai ga ƙin biyan ƙorafe-ƙorafen da ake da ƙalubale akansu da masu shigo da fetur suka miƙa, bayan haka aka yi awon-gaba da mahaifiyarta, Kemene Okonjo daga gidanta da ke yankin Ogwashi-Uku a Jihar Delta. A wata hira da aka yi da ita a kwanan nan, Shugabar ta WTO ta bayyana cewa masu garkuwar sun buƙaci ta ajiye muƙaminta na ministar kuɗi, sannan ta fice daga ƙasar a matsayin sharaɗin sako mahaifiyarta.

Okonjo-Iweala dai ita ce Ministar Kuɗin Nijeriya a tsakanin shekarar 2011 da 2015 a ƙarƙashin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Ebele Jonathan.

Ta bayyana cewa, al’amarin binciken tallafin ya fara ne bayan ofishinta ya gano cewa ana samun ƙarin ƙorafe-ƙorafe akai-akai da masu shigo da fetur ke miƙawa, lamarin da ya sa ta gaggauta neman amincewar Shugaba Jonathan akan ta fitar da bayanan asusu. A cewarta, bayan samun amincewar ne sai suka gano akwai biliyan $2.4 da aka sauya akalarsu, don haka suka ƙi biya, inda jim-kaɗan bayan sanar da matakin nasu ne sai aka sace mahaifiyar tata.

Tsohuwar ministar ta bayyana al’amarin a matsayin shiga halin ƙunci mafi muni a tarihin rayuwarta, inda ta ƙara da cewa an ajiye mahaifiyar ne a jeji na tsawon kwana biyar kana daga bisani ta samu tserewa a wani dare. “Har yanzu tana raye. Yanzu ta kai 96”, inji Okonjo Iweala.

Kazalika, ta ce da fari ta fara yunƙurin ajiye muƙamin nata, amma mahaifinta ya gargaɗe ta akan biye wa buƙatun masu garkuwar tare da ƙarfafa mata giwar cigaba da ƙoƙarin sauke nauyin da aka ɗora mata.

By Babaji

Leave a Reply