Tinubu ya nemi amincewar majalisa bayan aike mata sunayen manyan daraktocin NMDPRA shida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Bola Tinubu ya bayar da sunayen manyan daraktoci guda shida na Hukumar kula da Harkokin Gudanarwar Man Fetur ta Ƙasa (NMDPRA) ga Majalisar Dattawa domin tabbatar da naɗinsu.

Uku daga cikinsu da ma daraktoci ne yayin da sauran ukun kuma sababbin naɗe-naɗe ne, a cewar sanarwar da aka fitar a ranar Juma’a daga Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga. Yayin da aka tabbatar da su, za su yi aiki na tsawon shekaru biyar.

Waɗanda aka bayar da sunayen nasu domin sake naɗa su sune Abiodun Adeniji a matsayin Babban Daraktan Kuɗaɗe da Asusu; Ogbugo Kalu Ukoha a matsayin Babban Daraktan Tsare-tsaren Rabawa, Adana da Harkokin Siyarwa; da Mustapha Lamorɗe a matsayin Babban Daraktan Lafiya, Aminci, Muhalli da Al’umma.

Sababbin sunayen sune Mobolaji Tajudeen Musa a matsayin Babban Daraktan, Rijiyoyin Tacewa, Ƙaddamarwa da Lamuran Jigila, Ogechukwu Modie a muƙamin Babban Daraktan Gudanarwar Tattalin da Dabarun Tsare-tsare da kuma Said Abutalib a muƙamin Babban Daraktan Harkokin Haɗaka da Gudanarwa.

Tinubu ya roƙi majalisar dattawan da ta duba sunayensu tare da tantance su akan lokacin domin tabbatar da ci-gaba mai ɗore a harkokin hukumar da kuma ƙarfafa wa sanya ido a lamuran gudanarwarta.

Haka kuma, shugaban Nijeriyar ya amince da nadin Jumoke Gafar a matsayin sakatariya ga Kwamitin Amintattun hukumar kuma Mai bayar da Shawara kan Harkokin Shari’a har zuwa lokacin da za a kammala cika sharuɗɗan hukunce-hukuncen Sashe ne 46 na Dokar Masana’antar Fetur (PIA).

A watan Afrilu ne dai Shugaba Tinubu ya naɗa Abdullahi Umar a matsayin Babban Daraktan hukumar ta NMDPRA.

By Babaji

Leave a Reply