PSC ta ƙara wa manyan ‘yan sanda 3,800 muƙami, ta kai biyu mataimakin sufeto janar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da Harkokin ‘Yan Sanda a Nijeriya (PSC), ta sanar da ƙara wa sama da manyan jami’ai guda 3,800 matsayi, ciki har da mataimaka sufeto janar (DIGs) guda biyu, mataimaka sufeto janar (AIGs) guda 10 da kuma kwamishinoni ‘yan sanda (CPs) guda 17.

An amince da wannan ƙare-ƙaren matsayi ne a wani zama da hukumar ta gudanar a Abuja, ranar Alhamis biyo bayan ƙoƙarin jami’an yayin rubuta jarrabawar neman ƙarin matsayi da tantancewar baka. Shugaban PSC, Hashimu Salihu Argungu, ne wanda ya jagoranci zaman a cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’ar hukumar, Torty Njoku Kalu ya fitar.

Jami’an da aka ƙara wa matsayi zuwa DIG sune Olalu Adegbite, wanda shi ne Shugaban INTERPOL National Central Bureau a Abuja da Dankombo F. Morris, wanda shi ne Shugaban Zone 4 headquarters a Makurɗi, Jihar Benuwai.

Hukumar ta kuma ƙara wa kwamishinonin ‘yan sanda 10 matsayi zuwa AIG. Sun haɗa da Omosanyin Olusegun, Ogbodo Ugobueze, Ohagwu Felix Ndukwe, Taylor Lennox Olanrewaju, Regina Cosmas Udoette, Afolabi Wilfred Olutokunbo, Nwogoh Martin, Shetima Jauro Mohammed, Ibrahim D. Gotan da kuma Danjuma I. Yahaya.

Wasu jami’ai 17 kuma an ƙara musu matsayi zuwa kwamishina. Sun haɗa da Nache Bashir Liman, Sirajo Lawal Salihu, Ayeleye Adegboyega, Isiaka O. Salau, Usman Shaik Adamu, Aminu Maiwada Garba, Abdulkarim Musa Waziri da kuma Muhammad Yusuf Adamu. Sauran sune Sani Adamu Nufawa, Bello M. Adamu, Okezie Chikezie C., Aminu Usman Gusau, Abiodun Onuoha, Salisu Bello Fago, Adegoke A. Alani, Wuwa Auwal Muhammad da Benedict U. Agbo.

Wannan mataki ya kuma shafi jami’ai 85 da aka tura gaba daga mataimaka kwamishinan ‘yan sanda zuwa (ACPs) zuwa mataimaka kwamishina (DCPs), Cif Sufuritanda 49 zuwa ACPs, Sufuritanda 45 zuwa Cif Sufuritanda da kuma Mataimaka Sufuritanda (DCPs) 498 zuwa Sufuritanda. Rukunin da ya fi girma shi ne na Mataimaka Sufuritanda (ASPs) 3,218 zuwa muƙamin DSP.

Da yake taya su murna kan samun muƙamin, Argungu ya yi kira ga jami’an da su ɗauki wannan mataki a matsayin ƙarin nauyi akansu musamman wajen bai wa rayuua da dukiyoyin al’umma kariya tare da tabbatar da kiyaye doka da oda, yana mai cewa hakan ya dace da ƙarfafa musu gwiwa wajen ƙara hoɓɓasa yayin gudanar da ayyukansu.

By Babaji

Leave a Reply