Majalisar Dattawa ta bai wa Kano, Sakkwato da wasu jihohi huɗu wa’adin 15 ga Nuwamba kan kafa ’yan sandan jihohi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Dattawa ta bai wa majalisun dokokin jihohi shida da ba su amince da shawarar kafa rundunonin ’yan sandan jihohi ba wa’adin zuwa ranar 15 ga Nuwamba domin su bayyana matsayarsu, tana mai gargaɗin cewa duk jihar da ta gaza mayar da martani kafin wa’adin za a ɗauka a matsayin wadda ta ƙi amincewa da ƙudirin.

Rahoton News Point Nigeria ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan bayanin da Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya yi a zaman majalisar ranar Laraba, inda ya ce majalisun dokokin jihohi 30 cikin 36 sun amince da ƙudirin gyaran kundin tsarin mulki.

Duk da cewa amincewar jihohi 30 ta haura adadin kashi biyu bisa uku da kundin tsarin mulki ya tanada, wato jihohi 24, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya buƙaci a ƙara wa sauran majalisun jihohi shida lokaci domin su bayyana matsayarsu.

Akpabio ya ce duk majalisar dokokin jihar da ta gaza mayar da martani kafin ranar 15 ga Nuwamba, za a ɗauka cewa ta ƙi amincewa da ƙudirin.

“Ya kamata a ƙara musu lokaci. Mu ba su zuwa ranar 15 ga Nuwamba domin su mayar da martani,” inji shi.

Dukkan mambobin Majalisar Dattawa sun amince da wannan buƙata.

Tun da farko, Bamidele ya karanta sunayen jihohi 30 da majalisunsu suka amince da ƙudirin.

Jihohin sun haɗa da Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Borno, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Ogun, Ondo, Osun, Plateau, Rivers, Sakkwato, Taraba, Yobe da Zamfara.

Bamidele ya ce adadin jihohin da suka amince ya wuce abin da kundin tsarin mulki ya tanada na kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi 36, wanda ya yi daidai da jihohi 24.

Shugaban masu rinjayen ya bayyana cewa tsarin gyaran kundin tsarin mulkin ya ƙunshi matakai uku: amincewar Majalisar Dokoki ta ƙasa, amincewar aƙalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi, da kuma sanya hannun shugaban ƙasa.

Ya ce: “Amincewa da ƙudirin ya kamata ta fara ne a Majalisar Dokoki ta ƙasa, kuma an riga an kammala hakan. Sai kuma amincewar aƙalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi 36, sannan shugaban ƙasa ya sanya hannu domin kammala tsarin.”

ƙudirin gyaran kundin tsarin mulkin na 1999 yana neman samar da damar kafa rundunonin ’yan sanda na jihohi, a matsayin wani babban sauyi a harkar tsaro da zai rarraba ikon gudanar da ayyukan ’yan sanda, tare da bai wa gwamnatocin jihohi damar kafa da gudanar da nasu rundunonin.

Ana sa ran wannan shawara za ta taimaka wajen magance matsalolin da ake ganin tsarin rundunar ’yan sanda ta ƙasa mai iko daga tsakiya ke fuskanta, musamman wajen tunkarar matsalar rashin tsaro a al’ummomi daban-daban na ƙasar.

Tsarin gyaran kundin tsarin mulki ya tanadi cewa aƙalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi ne za su amince da ƙudirin kafin a miƙa shi ga shugaban ƙasa domin sanya hannu.

Yayin da majalisun jihohi 30 suka riga suka amince da ƙudirin, matakin Majalisar Dattawa na ƙara wa sauran jihohi shida wa’adi na da nufin ba su damar kammala nasu ɓangaren kafin a miƙa ƙudirin ga shugaban ƙasa domin duba shi.

By ukarofi

Leave a Reply