APC sai da taimakon jami’an tsaro take gudanar da kamfen a Katsina – Babba Kaita

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar ADC, Sanata Ahmed Babba Kaita, ya yi zargin cewa yanzu jam’iyyar APC sai ta nemi taimakon jami’an tsaro kafin gudanar da kamfen a wasu ƙananan hukumomin jihar.

Sanata Babba Kaita ya bayyana cewa duk lokacin da APC za ta kai kamfen wata ƙaramar hukuma, sai an tura DPO da jami’an DSS domin tattaunawa da lallashin jama’a kafin tawagar jam’iyyar ta shiga wurin.

Ya ƙara da cewa rikicin APC a yanzu ya wuce tsakaninta da ‘yan adawa, inda a cewarsa, rikicin ya koma tsakaninta da al’umma.

“Rikicin jam’iyyar APC a Jihar Katsina ba da ‘yan adawa bane, tsakanin ta da al’ummar jihar ne,” Inji Babba Kaita.

Sanata Babba Kaita wanda ya bayyana cewa a ranar Asabar mai zuwa zai ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe a garin Funtua,”ba zan sake ambatan jam’iyyar APC ba tunda bada su take rigima ba.

Ya ce ko zuwan su ƙaramar hukumar Kankiya inda nan ne mahaifarsa sai da shugaban ƙaramar hukumar ya kira sa yana roƙon arziki da ya lallaɓi ya’yan jam’iyyar mu ta ADC da mu ƙauracewa wurin da za su gudanar da kamfen domin gudun tashin hankali.

Babba kaita ya nuna takaici duk da ɗinbin kuɗaɗen da Jihar Katsina ta samu babu wani abin azo a gani da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta taɓuka,”kaje babban asibitin Kankia ba magani,”Kaita yace.

By ukarofi

Leave a Reply