Canjin kuɗi: Kotun Ƙoli ta tafi hutu

Daga WAKILINMU

Kotun Ƙoli mai sauraron shari’ar sauyin kuɗi tsakanin gwamnatocin jihohi 13 da Gwamnatin Tarayya ta tafi hutu.

Alƙalan kotun su bakwai ƙarƙashin Mai Shari’a Inyang Okoro sun ce sun tafi hutu domin bai wa lauyoyin ɓangarorin da ke shari’ar damar yin musayar takardu.

Hakan na zuwa ne bayan Jihar Ribas ta shiga jeri a matsayin ta 13 a cikin jihohin da ke ƙalubalantar sauyin kuɗin da gwamnati ta yi.

Tun da farko, Mai Shari’a Inyang Okoro, ya ce ya zama tilas kotun ta cimma matsaya a kan shari’ar a zamanta na yau.

Wannan shi ne zama na biyu da Kotun Ƙolin ke sauraron ƙarar da jihohin suka shigar kan Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Nijeriya (CBN) inda suke neman kotun ta hana ɓangaren gwamnatin aiwatar da wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kuɗin da aka sauya wa fasali, wato N200, N500 da kuma N1000.