2023: An tsinci gawar ɗan takarar gwamna cikin daji ta fara ruvewa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An tsinci gawar tsohon ɗan takarar gwamna a Jam’iyyar APGA a Jihar Enugu cikin daji.

Mamacin mai suna Dons Ude, ya fito takarar zaɓen fidda gwani a zaɓen gwamnan jihar na 2023 da aka kammala cikin Maris.

An tsinci gawarsa ce bayan an bayyana sanarwar vacewarsa tun a ranar Asabar.

An ce an tsinci gawar Ude daidai Kwanar Mil 9 da ke Ƙaramar Hukumar Udi, cikin Jihar Enugu.

An kuma tabbatar da cewa ita ma motarsa wadda ya ke ciki daga lokacin da aka neme shi aka rasa, an ganota.

Dama kuma tun da farko an yi ta kiran lambobin wayarsa, amma ba ya ɗauka.

Lamarin da ya jefa makusantansa cikin damuwa cewa ko an yi garkuwa da shi ne.

Majiyoyi sun ce an samu wayarsa jikin bangon ofishin ‘yan sanda na Ogui. Hakan ya sa an lara shiga firgici cewa lallai ya na cikin tashin hankali.

Daga baya an sanar da matarsa cewa an tsinci wayarsa.

An ce matarsa ta garzaya ofishin ‘yan sanda ta sanar da su cewa ta kasa samun lambobin wayar mijinta.

Har yanzu dai ba a sani ba ko masu garkuwa ne su ka sace shi.

Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Enugu, Daniel Ndukwe, ya tabbatar da mutuwar ɗan siyasar a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba da dare.

Ya ce an tsinci gawar ɗan siyasar bayan har ta ruve, a ranar Talata wajen ƙarfe 11 na dare a cikin daji, gefen titin Bypass.

Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan ya ce tun a ranar Asabar mamacin ya bar gida a cikin Enugu, inda ya fita cikin motarsa ƙirar Toyota Highlander SUV.

Ndukwe ya ce, “an ga raunuka a jikin gawar mamacin, abin da ke tabbatar da cewa an yi amfani da makami wajen lahanta shi, kuma ta hanyar ce aka kashe shi.”

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Enugu, Ahmed Ammani ya ce jami’an da dogon bincike.

Kakakin ya ce yanzu haka dai an ajiye gawarsa a ɗakin ajiye gawarwaki kuma ana ci gaba da bincike.