Raɗɗa zai tantace ma’aikatan gwamnati bayan an rantsar da shi

Daga UMAR GARBA a Katsina

Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dakta Dikko Umaru Raɗɗa, ya bayyana shirin gwamnatinsa na gudanar da tantance ma’aikata a ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar 34, bayan rantsar da shi a matsayin gwamna a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Raɗɗa wanda ya gabatar da tambayoyi a lokacin wani shirin talabijin, ya nuna rashin jin daɗinsa da wasu ma’aikatan duk da cewa suna cikin tsarin biyan albashi na gwamnati har yanzu ba su da wani tasiri wajen bayar da hidima.

“Abin da muke so mu yi shi ne, tantance ma’aikata sosai idan muka zo don tabbatar da cewa mutanen da ke kan albashin suna ba da ayyuka ga ƙananan hukumomi.

“Abin takaici sai ka ga wani yana karɓar albashi a ƙaramar hukuma, amma ya riga ya samu aiki a matakin tarayya ko kuma wasu kamfanoni masu zaman kansu sai ya riqa karvar albashi biyu don aikin bai yi ba.

“Don haka, muna buqatar mu fitar da waxancan abubuwan,” inji shi.

Raɗɗa ya bayyana aniyarsa ta bai wa ƙananan hukumomin dama don gudanar da kuɗaɗensu, inda ya qara da cewa gwamnatinsa za ta kafa wata hukuma mai inganci ko ma’aikatar da za ta tabbatar da bin diddigin duk wani kashe kuɗi.