TinT da IBP sun horas da mutum 34 batun biyan haraji a Kano

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Ƙungiyar bibiyar haraji da akafi sani da Follow Taxes ko T in T tare da haɗin gwii IBP ta shirya mlwa mata da maza bita a kan abin da ya shafi haraji a jihar Kano.

Wannan taro na zuwa ne adaidai lokacin da mafi yawan jama’a ke kokawa da irin ƙalubalen da ke ci wa al’umma tuwo a ƙwarya kan batun haraji a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Da yake yi wa mahalarta taron ƙarin bayani, ɗaya daga cikin masana dangane da batun haraji a jihar Kano kuma Shugaban kungiyar wanzar da zaman lafiya da samar da domukuraɗiyya mai ɗorewa, wato DAG, DR. Mustapha Muhammad Yahaya, ya ce wannan taro zai taimaka wa musamman mata wajen sanin menene ma harajin.

Dr. Mustapha Muhammad wanda shi ne ko’odinatan Tax Justice a jihar Kano ya ƙara cewa, mafi yawan mata suna da ƙarancin sani kan waɗanda ya kamata a ce sun biya haraji ta wannan bita za su samun ƙarin haske da abin da ya kamata a ce suna yi.

Ya kuma shaida cewa Ƙungiyar (IBP), watau International Budget Partnership, ta fi ba mata mahimmanci dan irin yadda ake karɓar haraji da yawa daga gurin su, hakan nan ya ƙara bayyana cewa mata sun fi faɗawa cikin wannan matsala.

Ita ma Mrs Madam Chika, ta ce wannan shirin yana ɗaya daga cikin ayyukansu don duba yanayin da mata da wasu mazan suke biyan haraji a ƙananan Kasuwancinsu ba tare da fahimtar su wa da kuma ina ya kamata su biya.

Madam Chika ta ƙara da cewa, kodayaushe masu biyan haraji su sani idan suka biya haraji ne gwamnati take da damar yi wa al’umma aiki da wannan kuɗin shiga da ake biya, madamar mutane ba su biya ba ba su da hujjar tuhumar gwamnati kan wannan batun.

Kazalika, ta ce kasancewar Jihar Kano tana daga cikin ƙungiyoyin mata ‘yan kasuwa da yawa yana ɗaya daga cikin dalilan da ya sa suka kawo wannan bita a nan don cimma manufa.

A cikin waɗanda suka halarci taron bitar sun haɗar da ƙungiyoyin mata ‘yan kasuwa na Jihar Kano da sauran ƙungiyoyin haraji na Jihar Kano gami da mata masu nakasa da masu ruwa da tsaki.

Daga ƙarshe, an gabatar da muƙalu daban-daban kan abin da ya shafi haraji da sauran su, an kuma gudanar da taro na kwana uku a ɗakin taro na Quarter House a Tamandu Road cikin ƙaramar hukumar Nasarawar jihar Kano.