‘Yan sanda sun kama mutum biyu da suka birne tsoho da ransa a Jihar Binuwai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwai sun kama wasu matasa biyu da suka kashe wani tsoho Ihwakaa a ƙauyen Ikyve dake Ƙaramar Hukumar Konshisha.

Ihwakaa ya gamu da ajalinsa bayan matasan ƙauyen sun zargesa da tsafi.

Wani mazaunin ƙauyen da baya so a faɗin sunansa ya ce rikicin ya somo ne bayan zarginsa da kashe ɗan Ihwakaa mai suna Henry, sirikarsa da jikarsa jaririyar a rana ɗaya.

Mazaunin ya ce ba tun yanzu ba mutanen ƙauyen na zargin tsohon da yin amfani da ruwa a ƙauyen domin yin tsafi da mutane.

“A dalilin haka ya sa matasa suka birne tsohon a rami da ransa domin a ganinsu waɗannan mutane uku sun mutu ne saboda tsafin da tsohon ke yi.”

Wani dattijo a ƙauyen mai suna Baba Agan ya ce duka dattawan ƙauyen za su zauna domin kada tarzomar ta wuce gona da iri.

“Babu daɗi abin da mutane suka yi na yin gaggawar ɗaukar doka a hannunsu ba tare da sun kira jami’an tsaro ba.”

Bayan haka kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Catherine Anene ta ce sun kama mutum biyu da ake zargi da hannu a aikata wannan mummunar abu.