Haaland ya kafa tarihin yawan jefa ƙwallo a gasar Firimiyar Ingila

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ɗan wasan gaba na Ƙungiyar Manchester City Erling Haaland ya kafa tarihin yawan cin ƙwallaye a gasar Firimiyar Ingila, inda a wannan kaka ya zura ƙwallaye 35.

Ɗan wasan wanda ɗan asalin ƙasar Norway ne, ya zarce yawan qwallaye 34 da ’yan wasa Alan Shearer da kuma Andrew Cole suka ci a gasar.

Bayan tashi daga karawar da su ka yi da West Ham a gasar Firimiyar Ingila, ‘yan wasan City sun jeru don jinjina wa ɗan wasan bisa bajintar da ya yi.

Haka nan ƙungiyar ta Manchester City ta samu nasarar jefa ƙwallo ta dubu 1 a ƙarƙashin jagorancin Pep Guardiola.

Baya ga hakan kuma, ƙungiyar ta sake taddo tarihin lashe wasanni 9 a jere a gasar da ta kafa tarihin hakan a baya, sannan kuma ta samu nasarar lashe wasa 14 daga cikin 15 na dukkanin gasanni da ta yi a baya-bayan nan.