Abinda ya sa muka kafa Kwalejin Marubutan Hausa – Kabiru Yusuf Fagge

“Rubutu a kafafen sadarwa na zamani cigaba ne”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

Duniyar marubutan adabi ba za ta taɓa mantawa da sunan Malam Kabiru Yusuf Fagge ba, wanda aka fi sani da ANKA, da irin gudunmawar da ya bayar kuma har yanzu yake kan bayarwa a harkar rubutun adabi, kama daga rubutun zube, wasan kwaikwayo har zuwa rubutun littattafan ýan makaranta, don bunƙasa ilimin yara manyan gobe. Marubuci, mawallafi, malamin makaranta, kuma ɗan kasuwa. Wakilin Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya yi kaciɓis da shi a Kano, bayan yayen ɗalibai zangon farko na Kwalejin Marubutan Hausa da aka gudanar, bayan kammala samun horon da suka yi a kan ka’idojin rubutun Hausa. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: Malam, ko za ka gabatar mana da kanka?
ANKA: Sunana Kabiru Yusuf Fagge wanda aka fi sani da Kabiru Anka. An haife ni a unguwar Fagge. Ni ɗalibi ne a Jami’ar Bayero ta Kano, a fannin nazarin harshen Hausa, kuma marubucin littattafan zube da wasan kwaikwayo da na ilimin firamare da sakandire.

Wacce gwagwarmaya aka yi a fagen neman ilimi, kuma yanzu a wanne mataki ka ke?
Na yi karatun Alƙur’ani da sauran littattafai tun daga karatun allo har zuwa saukar karatun Alƙur’ani. Sannan a fannin boko, na yi karatu a fannin ‘Statistics’ da ‘Computer’ a matakin Diploma da karatu a kan shirya finafinai wato ‘Film production’ a makarantun IFBA Lagos da ‘Northwest University’ shi ma a matakin Diploma, kafin in sauya layi, in koma nazarin harshen Hausa, inda har yanzu nake ɗalibta.

Tsawon wanne lokaci ka shafe a harkar rubutun adabi, kuma wacce gudunmawa ake bayarwa har yanzu?
Na shafe tsawon shekaru 26 ko fiye. A yanzu ina bayar da gudummawa kan harkar rubuce-rubucen zube ne ta fuskoki da dama, ciki har da buɗe makarantu don koyar da marubuta dabarun rubuce-rubuce da yin bitoci a dandalin marubuta daban daban, da kuma samar da littattafai da za su taimakawa marubuta inganta rubutun su. Haka nan da yin ruwa da tsaki don ganin matasan marubuta masu tasowa sun tallafi harkar rubuce-rubuce ka’in da na’in.

Kawo yanzu littattafai nawa ka wallafa ko kuma ka ke aiki a kansu?
Na wallafa littattafan zube sama da goma sha shida. Na wasan kwaikwayo guda 3. Na koyar da Turanci ko haruffan Turanci ko lissafi musamman na yara guda 12. Akwai kuma na ban dariya guda 6. Haka kuma ina cikin littattafan haɗaka na marubuta guda 3. Daga cikin littattafan da na bayyana kamar na zube akwai, ‘Ƙarfin Hali’, ‘Shure Shure’, ‘Ninƙaya’, ‘Alwashi’, ‘Bilkisu’, ‘Firgita Samari’, ‘Rayya’, ‘Yanmata’, ‘Kushewar Baɗip, ‘Launin So’, sai kuma ‘Ya’yanmu da Tatsuniyoyi Da Labarun Gargajiya’. Kuma har yanzu dai ina kan ayyukan wasu manya-manyan littattafai na zube. Alhamdulillah! 

Wanne irin cigaba ko koma baya za ka iya cewa an samu a wannan harka ta rubutun adabi?
Akwai cigaban da aka samu sosai. To, amma rashin wayewa da zamani yana neman ya zama ci baya gare mu marubuta. Farko matsalar tattalin arziƙi ta kawo ci baya a harkar rubutu. To, amma zuwan ci gaban zamani ta kafafen sada zumunta irin su facebook, WhatsApp da sauransu, sun kawo ci gaba a harkar. Amma rashin bin cigaban nan yana neman mayar da shi ci baya ga wasu marubutan. 

Wanne ƙoƙari kuke yi na ganin an farfaɗo tare da inganta harkar rubuce rubuce a harshen Hausa?
Kamar yadda na faɗa a baya, ta hanyar wayar da kan marubuta muke son farfaɗo tare da inganta harkar rubuce-rubucen Hausa ta yadda zai riƙa gogayya da ci gaban zamani.

Wacce gudunmawa marubutan zube suke bayarwa ga harkar shirya finafinan Hausa?
Ai marubutan zube su ne harkar finafinan Hausa. Don haka su suka bayar da gudunmawar samuwar harkar kuma su ne suke ba ta gudunmawa take bunƙasa.

Kana daga cikin shugabannin makarantar Kwalejin Marubutan Hausa da aka kafa, mene ne manufarku ta yin haka?
Manufar samar da makarantar don fito da haziƙan marubuta ne da ba a san su ba, da kuma samar da inganci a rubutun da suke yi, da kuma samar da marubutan da za su ciccivi harkar rubutun su kai ta wani babban matsayi daga yanzu har zuwa nan gaba. Kuma Alhamdulillahi a karon farko kwalliya ta biya kuɗin sabulu, da yawan marubutan da suka yi karatun nan su suke yin zarra a gasa da sauran al’amuran rubutun Hausa.

Bangon littafin ‘Ya’yanmu

Kun yaye rukunin ɗalibai nawa, kuma wacce nasara hakan ya kawo ga harkar rubutun adabi?
Wannan shi ne karo na farko da muka yaye, kuma an samu gagarumar nasara wanda har ta kai Farfesan da ya daɗe yana yi wa adabi hidima Farfesa Yusuf Adamu ya jinjina tare da tabbatar da cewa wannan abu ya ƙara wa adabi matsayi na musamman. Alhamdulillahi! 

Yaya ka ke kallon komawar rubutun adabi a kafafen sadarwa na zamani, a maimakon littafi na takarda da a baya aka san ku a kai?
Rubuce-rubuce a kafafen sadarwa na zamani cigaba ne, kuma ni ina maraba da shi, musamman idan za a yi da tsari da inganci. Haka nan adana rubutu a littafi kusan yana kan gaba wajen abin da ya fi dacewa. Wannan ci gaba ne sosai.

Yaya alaƙar ku a matsayin ku na tsofaffin marubuta, da matasa na yanzu masu tasowa da ke rubuce rubuce a ‘online’?
Mu da marubuta masu tasowa ‘yan’uwan juna ne. Ni ba na bambamcewa, duk ɗaya muke. Idan ka ga na bambance to, ka tabbatar marubucin ya yi rubutun da bai dace ba, a nan ne nake bambanta kaina da irin waɗannan marubutan. 

Wanne hange kake da shi nan gaba a harkar rubutun adabi a Arewa?
Harkar ta kai wani mataki da a ko’ina za ta yi tasiri. Idan na ce ko’ina ina nufin tun daga harkokin siyasa da gwamnati da zamantakewa da duk wasu harkokin cigaban rayuwa. Mu zama abin alfahari da tunawa.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwar ka?
Kiɗa a ruwa mai tada hankalin dodo!

Mun gode.
Ni ma na gode.