Mahangar Xi Jinping game da babbar manufar jagoranci

Daga SAMINU HASSAN

A tsawon shakaru masu yawa, masana da ƙwararru, da masu dinbin basira a sassan rayuwa daban daban na ƙasar Sin, sun sha tattaunawa game da ainihin babbar manufar jagorancin ƙasa, ko abu mafi muhimminci ga kowace irin ƙasa. Daga ƙarshe dai, a kan rinjayar da ginshikai kamar tsaro, da managarcin tsarin siyasa, ko kuma gogewar jami’an dake jagorantar sassan hukumomi.

To amma ga shugaban ƙasar Sin Xi Jinping, amsar ita ce, sanya al’ummar ƙasa cikin yanayi na farin ciki. Hakan ne ma ya sa, a yayin da yake ziyarar aiki a lardunan ƙasar Sin, ya kan ziyarci gidajen talakawa a yankunan karkara domin sanin halin da suke ciki.

Ga misali, a shekarar 2013, shugaba Xi ya ziyarci ƙauyen ’yan ƙabilar Miao dake sassan tsaunukan lardin Hunan. A wancan lokaci ya shiga gidajen talakawa, inda ya buƙaci sanin irin nau’o’in abinci da ’ya’yan itatuwa da suke iya samu domin rayuwa.

A lokacin da yake matashi, Xi ya shafe tsawon shekaru 7 a ƙauyen Liangjiahe na lardin Shaanxi, wurin da a lokacin ƙauye ne maras wadata. Bayan ganewa idanunsa halin ƙunci da al’ummu mazauna yankunan tsaunuka ke rayuwa a ciki, shugaban na Sin, ya ƙuduri aniyar bauta wa jama’a, da tabbatar da rayuwar su ta kyautata.
Ya kuma cimma wannan buri, ta hanyar zaburar da ɗaukacin sassan jagororin ƙasar, game da buƙatar sanya jin daɗin jama’a gaban komai.

Ko shakka babu, wannan ƙwazo na shugaba Xi ya haifar da ‘da mai ido, domin kuwa, a yayin wata ziyara da ya kai ƙauyen Wang Deli dake yankin tsaunukan lardin Guangxi a bazarar shekarar 2021, ya zanta da wani magidanci, wanda ya ce masa “Shugaba kana shan aiki, amma duk da haka ka yi ƙoƙarin ziyartar mu. Muna matuƙar godiya”.

Da jin haka sai shugaba Xi ya ce masa “To ai wannan ne aikin da na sanya gaba.” A mahangar shugaba Xi, sanya al’umma farin ciki shi ne babban aikin duk wani shugaba.

Ko shakka babu, wannan manufa ce mai cikakkiyar ma’ana. Domin kuwa ba wata al’umma da ba ta fatan yin rayuwa cikin farin ciki!