Adadin ‘yancin mallakar fasaha da suka samu amincewa a Sin ya kai miliyan 4.081

Daga CMG HAUSA

Yau ne, hukumar kula da ‘yancin mallakar fasaha ta ƙasar Sin ta shirya taron ganawa da manema labarai mai laƙabin “Kare ‘yancin mallakar fasaha a cikin shekaru goma da suka gabata”, inda mataimakin shugaban hukumar Hu Wenhui ya bayyana cewa, aikin kare ‘yancin mallakar fasaha ya samu babban sakamako a cikin shekaru goma da suka gabata, tun bayan da aka kira babban taron wakilan JKS karo na 18 a shekarar 2012.

A cikin waɗannan shekaru goma, adadin ‘yancin mallakar fasaha na ƙasar Sin ya karu, kuma ingancinsu ya kyautata.

Ya zuwa watan Satumban bana, gaba daya adadin ‘yancin mallakar fasaha da suka samu amincewa a ƙasar ya kai miliyan 4.081, kuma matsayin ƙasar Sin a jerin sunayen “Rahoton alƙaluman ƙirƙire-ƙirƙire a faɗin duniya” da hukumar kare ‘yancin mallakar fasaha ta duniya ta fitar ba da daɗewa ba, ya ci gaba daga matsayi na 34 na shekarar 2012 zuwa na 11 a shekarar 2022, wato matsayin ƙasar Sin ya ci gaba da daguwa a kai a kai a cikin shekaru goma da suka gabata, musamman ma ta fuskar ƙirƙire-ƙirƙiren kimiyya da fasaha.

Hakazalika, saurin amfani da ‘yancin mallakar fasahar ƙasar Sin ya ƙaru a cikin shekaru goma da suka gabata, gaba ɗaya adadin lambobin zinariya da aka bai wa ɓangaren ‘yancin mallakar fasahar ƙasar ya kai 310, waɗanda darajarsu ta kai kuɗin Sin yuan triliyan 2.5.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa