Wakilin Sin ya yi cikakken bayani kan sakamakon da Jihar Xinjiang ta samu wajen kare haƙƙin bil Adam

Daga CMG HAUSA

A yayin taro karo na 51 da hukumar kare haƙƙin bil Adam ta MƊD ta kira kwanan baya, wakilin ƙasar Sin ya yi cikakken bayani kan babban sakamakon da jihar Xinjiang ta samu a wannan ɓangaren, inda ya yi nuni da cewa, jihar Xinjiang ta ƙasar Sin tana ɗaukar batutuwan da suka shafi jin daɗin rayuwar jama’a a matsayin haƙƙin bil Adam mafi muhimmanci bisa ƙa’idar martaba da tabbatar da haƙƙin bil Adam kamar yadda kundin dokokin ƙasar suka tanada, kuma ta ciyar da sha’anin kare haƙƙin bil Adam gaba ta hanyar ɗaukar matakan kyautata rayuwar al’ummar jihar.

An lura cewa, a jihar ta Xinjiang, duk da cewa, akwai bambancin adadi tsakanin ƙabilun jihar, da yanayi na tarihi, da matsayin samun ci gaba, da kuma al’adu, amma al’ummu ‘yan ƙabilu daban-daban dake jihar, suna zaman jituwa ne bisa matsayi na daidai wa daida, kuma suna tafiyar da harkokin ƙasa da jihar tare, da ma jin dadin rayuwarsu tare yadda ya kamata.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa