AFCON 2025: Super Eagles ta fara da ƙafar dama bayan doke Tanzaniya a rukunin C

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Super Eagles ta Nijeriya ta bi sawun sauran manyan ƙasashe wajen fara gasar AFCON da ƙafar dama sakamakon doke Tanzaniya a wasanta na farko da ci 2 da 1.

‘Yan wasa Semi Ajayi da Ademola Lookman ne suka zura wa Super Eagles ƙwallayen da suka ba tawagar Nijeriyar nasara.

Da fari, ɗan wasa Alex Iwobi ne ya yi bugun tazara daga gefen fili, wands hakan ya ba Semi Ajayi damar zura ƙwallon farko a wasan.

Tanzaniya ta samu damar farkewa ne yayin da aka dawo hutun rabin lokaci da mintuna biyar ta hannun ɗan wasanta mai suna Charles M’Mombwa.

Saidai duk da haka, Nijeriya ta yi nasarar zura ƙwallo na biyu a lokacin da Ademola Lookman ya samu dama jim-kaɗan da farkewar Tanzaniya.

An buga wasan ne tsakanin ƙasashen biyu, wanda shi ne na farko a gasar cin kofin Afirka ta 2025 da ake gudanarwa a ƙasar Moroko.

Najeriya za ta yi wasanta na biyu da ƙasar Tunisiya a birnin Fes a yammacin ranar Asabar.

Ita kuma Tanzaniya za ta yi karawa ta biyu da Uganda a birnin Rabat a ranar ta Asabar ita ma da yamma.

By Babaji