AFCON: Buhari ya taya ‘yan wasan Super Eagles murna

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya bayyana jin daɗinsa tare yaba wa ‘yan wasan Super Eagles dangane da nasarorin da suka samu a duka wasanni ukun da suka buga a gasar cin kofin Afirka (AFCON) da ke gudana a ƙasar Kamaru.

Buhari ya nuna jin daɗinsa ne a saƙon da ya wallafa a shafinsa na facebook a ranar Laraba.

Buhari ya buƙaci ‘yan wasan da su ci gaba da tabbata a kan wannan hanya ta nasara da suka ɗauka har zuwa ƙarshen gasar tare kuma da zama jakadu nagari ga Nijeriya a cikin filin wasa da kuma wajen fili.

Shugaba Buhari ya shaida wa ‘yan wasan cewa ‘yan Nijeriya sun ɗora musu fatan lashe duka wasanni bakwai da za su buga, wanda sun bugu wasanni uku yanzu saura huɗu.

Shugaban ya tabbatar da bada cikkaken goyon bayansa ga ‘yan wasan don ƙarfafa musu gwiwa wajen buɗe wani sabon shafin tarihin ƙwallon ƙafa a Nijeriya.