Matsalar tsaro: Laifin gwamnati ko na al’umma? (1)

Daga NAFI’U SALISU

Da sunan Allah Mai rahama, Mai jinƙai.

Matsalar tsaro, wani al’amari ne da ya ɗauki dogon lokaci yana ci wa al’umma tuwo a ƙwarya, musamman a yankin Arewacin ƙasar nan. Domin kuwa hatta ƙananan yara sun fahimci halin da ƙasa take ciki a kan rashin tsaro. Sai dai kuma wasu al’umma suna danganta laifin matsalar tsaro kacokan a kan Gwamnati, wanda hakan ya haifar da tsana mai tsanani, da faɗar baƙaƙen maganganu marasa daɗin ji a bakunan al’umma ga su shugabanni. Haka kuma wasu kan danganta matsalar rashin tsaron a kan al’umma da kuma Gwamnati.

To masu iya magana sun ce; “Idan an bi ta ɓarawo, dole a bi ta ma bi sawu.” Domin kuwa, “Idan ɓera da sata, to daddawa ma da wari.” Al’umma su ma suna da rawar da za su taka a kan magance matsalar tsaro da ya addabi ƙasar nan, musamman ma yankin Arewa. A yau al’ummar Arewa sun sauya ba irin al’ummar baya ba, waɗanda suke tsayawa kai-da-fata wajen kula da tarbiyyar iyalansu a gida da waje. Mun sani cewa, Malam Bahaushe da ya fito daga yankin Arewacin ƙasar nan, mutum ne wanda yake da kyawawan al’adu, waɗanda tun lokacin jahiliyya ba duka ne suka kasance gurɓatattu ba. Domin Hausa-Fulani an san su da kunya, kara da addini.

Idan muka koma baya a cikin ƙarnin da ya gabata kafin wannan da muke ciki (ba sai mun koma baya sosai ba), za a ga cewa, hatta yaron maƙwabcinka idan ya yi laifi ba sai mahaifinsa ko mahaifiyarsa sun hukunta shi ba, kai a matsayin ka na maƙwabci za ka iya hukunta shi dai-dai da irin laifin da ya aikata. Sannan idan iyayensa suka samu labarin abinda ya yi na ba dai-dai ba, su ma za su ƙara hukunta shi, sannan kai a matsayinka na maƙwabci da ka tsawatar a karon farko, har gida iyayen wancan yaron da ya yi laifi za su zo su yi maka godiya. To kun ga a nan shi yaron zai fahimci cewa, da iyayensa da kai maƙwabci duk ɗaya ne, tunda yayi laifi ka hukunta shi kuma iyayensa sun ƙara yi masa wani hukuncin (ba su yi faɗa, ko ganin an yi laifi a kan hukuncin da aka yi wa ɗansu). Saɓanin haka, sai suka nuna masa abinda ya yi ba dai-dai ba ne. Kai kuma da ka hukunta shi, sun ji daɗi, kuma ka yi musu dai-dai. To a nan shi yaron zai ji tsoron sake yin wani laifin ko a bayan idon iyayensa ne. 

Wannan yana nuna irin yadda a ke bai wa ‘ya’ya cikakkiyar tarbiya, saboda ana nuna musu girman na gaba da su, da kuma muhimmancin abota da zaman maƙwabtaka da ake yi da mutanen da ba su ne iyayenka ba.
To, amma yanzu al’amarin ba haka ya ke ba, saboda a yanzu maƙwabcinka yana kallon ɗanka ko ‘yarka suna aikata ba daidai ba, amma ba zai yi magana ta tsawatarwa a kai ba. Dalili kuwa shi ne, idan ya yi magana su yaran za su tsane shi, ko su yi masa rashin kunya. Idan ya zo ya samu mahaifin yaron ya faɗa masa ga irin abubuwan da yake yi na assha, to sai ka ga uban yaro ko uwa sun ɗauki abin a matsayin baƙin ciki a kan ɗansu ko sa-ido. Hakan yana haifar da faɗa ko rashin jituwa a tsakanin mutane. Saboda iyayen ba sa son abin da zai ɓata wa ‘ya’yansu rai, ko faɗa yara suka yi a junansu a cikin unguwa, to iyaye su kan shiga har gidan maƙwabta a yi dambe (da sunan sun shigar wa ‘ya’yansu sun tare musu faɗa). To a nan me iyaye suke nuna wa ‘ya’yansu? Abinda suka aikata aka tsawatar musu daidai ne ba laifi suka yi ba. su kuma yaran sai su riƙa kallon maƙwabta a matsayin ‘yan sa ido, munafukai. 

Wannan shi ne ummul’aba’isin kawo rashin jituwa tsakanin maƙwafta. Al’umma su riƙa faɗa a tsakaninsu saboda yara, su ma yaran su riƙa faɗa da junansu har ɗaya zai iya cire makami ya soki ɗan’uwansa. A sakamakon haka, ana yi wa juna munanan raunika. Wasu lokutan ma har a rasa rai.

 Daga nan sai iyaye su fara gaba, su ma yara gaba. To ire-iren waɗannan abubuwan suna taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar al’umma.

Idan za a iya tunawa, a zamanin baya za ka ga yara matasa suna girmama junansu saboda kyakkyawar zamantakewa, haka ƙananun yara suna girmama duk wani babba. Idan yaro ya hango abokin mahaifinsa yana tahowa, shi kuma yana tare da abokansa, sai ka ji ya ce, “ga abokin Babanmu nan,” duk sai sauran yaran kowa ya nutsu. Da zarar ya iso daf da su, sai ka ga sun zube ƙasa suna gai da shi Haka nan idan wasan banza suke yi, to ko maƙwafcinsu suka gani sai sun daina. Matan Hausawa ba sa iya fita unguwa sai duhun Magriba ya shigo, kuma da shiga ta kirki, ta kamala ba irin ta yanzu ba. Haka nan idan suka biyo hanyar da maza ke zaune suna hira, to sai dai su canza hanya. Hakazalika, duk iyayen da Rana ta faɗi suka duba suka ga ɗansu bai dawo gida ba, to hankalinsu zai tashi. Da zarar ya dawo kuma za su tuhume shi ina ya je? Me ya tsai da shi har dare? Wanda kun ga savanin yanzu da ba ma wai ɗa namiji ba, ‘ya mace (budurwa baliga) sai ta fita ta kai dare waje ba ta gida, amma iyayenta ba su damu da su neme ta su ji tana ina ba, mafi yawancin iyayen yanzu haka suke. Wasu yaran ma kwana suke a waje, idan aka tambaye su, sai su ce gidan qawa suka kwana. waɗannan waɗanda ake saka ido ma a kansu kenan.

Don haka, lalacewar tarbiyya da sakacin iyaye tabbas ya taka muhimiyyar rawa wajen lalacewar zukatan ‘ya’ya (musamman matasa). Kuma a yanzu halin da a ke ciki, wasu ‘ya’yan sun koma tamkar su ne iyayen, iyaye kuma sun dawo su ne tamkar ‘ya’yan, sai ka ga uwa ko uba suna fama da ‘ya’ya (musamman maza matasa) a kan su daina shirme da shashanci, su nutsu su kama kansu. Amma sai ka ga ‘ya’yan har akan samu wasu da suke yin fushi da iyayen a kan suna yi musu faɗa. Wasu iyayen kuma idan suka yi faɗan suka ga ran yaro ya ɓaci, sai kuma ka ga sun dawo suna rarrashinsa. To wannan ma wani nau’i ne na taɓarɓarewa da lalacewar tarbiyya. 

Ni da kaina naga matashin da ya tara gashi a kansa, har gashin ya koma tamkar irin kitson nan da ake yi wa yara a ɗaure musu gashi curi-curi da robar kitso, (shi ne naji ana kira da sunan Dada), shi wannan matashin wallahi Hausa-fulani ne. Kuma kakanni da iyaye duk Musulmi, shi ma Musulmi. Amma idan ba ka san asalinsa ba, idan ka gan shi wallahi za ka ce masa shi ba ɗan musulmi ba ne, ɗan arna ne. 

Kwaikwayon al’adun wasu:
Tabbas kwaikwayon al’adun wasu mutane da ba jinsinmu na Hausawa ba, ya taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar tarbiyyar matasanmu, wanda hakan ya haifar da shigar wasu da yawa daga cikinsu cikin ayyukan ta’addanci. Wanda a yanzu irinsa ne yake addabarmu. Sai ka ga matashi ɗan musulmi, amma shigarsa irin ta kafirai, kansa ya ajiye gashi irin yadda kafirai suke yi (kuma kafiran ma marasa ɗa’a. Domin a cikinsu akwai masu ɗa’a da jin kunya gami da kamewa). Su kuma marasa kunyar ko a can ƙasashensu tatattun tantirai ne. Amma sai ka ga ‘ya’yan musulmi suna kwaikwayonsu. Kwaikwayo a magana, kwaikwayo a saka suttura, kwaikwayo a tafiya, kwaikwayo a mu’amala ta yau-da-kullum, da sauransu.

Ire-iren waɗannan abubuwan suna ɗaya daga cikin abinda ya kawo rashin tsaro a ƙasa, domin matasan da ya kamata a ce sun tallafa da ƙarfinsu, da jininsu, da basirarsu ƙasa ta ci gaba, amma sun zama lalatattu, wasu har da samun goyon bayan iyayensu.

Tasirin lalacewar tsaro daga ɓangaren gwamnati:
Idan muka koma kan Gwamnati, za mu lura da wasu abubuwa da suka taimaka wajen lalacewar al’umma, wanda shi ne dalilin rashin samun zaman lafiya a ƙasa. Kuma hakan ya jawo aka kassara wani yanki, yayin da shi kuma ɗayan yankin suke neman a raba ƙasar. Dalili, saboda sun hango abin da suka hango, wanda daga ciki akwai rashin iya shugabanci da jagoranci na mutanen Arewa. Ina magana ne a kan shugabannin Arewa da Allah yake ba su ikon tafiyar da mulki a hannunsu. 

Akwai abubuwa da dama da ya kamata a ce duk wani shugaba yana tunawa da shi, shi wannan abin ba komai ba ne face al’ummar da yake mulka. A matsayinka na shugaba a cikin gidanka ma ya ka ƙare, ballantana shugabancin al’ummar ƙasa? Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Kowanne mutum makiyayi ne (a gidansa da harkokinsa da al’umma), ranar Alƙiyama kuma za a tambaye shi game da wannan kiwon nasa.” Kun ga kenan duk wani magidanci da yake da iyali, wajibi ne yayi taka-tsan-tsan wajen kula da haƙƙin iyalinsa, domin ranar Alƙiyama za a tambaye shi game da yadda ya kula da su.

Hakazalika, shugaba mai mulki. Domin Allah Shi da kansa ya ce Ya hana wa kansa zalunci, kuma ya hana shi a tsakanin mutane (bayinSa). Don haka, akwai abubuwa da dama da rashin samar da su a tsare da kuma a aikace zahiri da baɗini, ya jefa ‘yan ƙasa cikin ruɗani da tashin hankalin da har yanzu ba mu san ya za mu ƙare ba. Za mu cigaba a mako mai zuwa idan Allah ya yarda. 

Nafiu Salisu
Marubuci/Manazarci.
[email protected]
[email protected]
08038981211