Aikata istimna’i a likitance (masturbation)

Tare da MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

Gabatarwa

Istimna’i hanya ce da mace ko namiji ke bi, domin biya wa kansu buƙata ta sha’awa ta hanyar shafar zakari ko farji da hannu kosandararrun abubuwa har sai su kawo.

Dabi’a ce mai illa ga lafiya sosai, amma kuma abin takaicin shi ne yadda kafofin intanet suka cika da bayanai akan alfanun yin istimna’i ba tare da mayar da hankali ga illolin da ya ke haifarwa a jik  ba. 

A lokacin da na ce zan fara gabatar da rubutu akan wannan maudu’i, wani ya tambaye ni ko shin akwai alfanu a cikin yin zinar hannu tun da komai da ka sani yana da amfaninsa da kuma akasin haka? Sai na ba shi amsa da cewa, tabbas ya na da alfanu, amma fa matsalolin da yake haifarwa sun fi alfanun yawa. Kamar dai khamru uwar laifi, yadda Alƙurani ya gaya mana cewa, illolinta sun fi alfanunta yawa.

Wasu daga cikin amfanin yin istimna’i sun haɗar da: gamsar da kai, sauƙaƙe tsananin sha’awa, sannan wataƙila zai sa a samu bacci mai daɗi. Bayan waɗannan, ni ban san amfaninsa a jiki ba. Abinda na damu shi ne, binciko matsalolinsa, domin sanar da alummata. 

Illolin wannan ɗabi’a a jiki sun haɗar da illata tsarin tsokar naman jiki, hanyoyin zagayawar j ni, ƙasusuwan jiki, jiyoyinjiki, fatar jiki (musamman fatar al’aura) da kuma cibiyar sarrafa jiki (ƙwaƙwalwa da laka).

Cikin yardar Allah, zan bi kowanne daki-daki na kawo bayanan illolinsa a rubutu mai zuwa, alabasshi daga baya na kawo muku hanyoyin da za a bi, domin dainawa da kuma abubuwan da za ku yi idan ya riga ya haifar muku da matsala.

Asalin istimna’I ke nufi?

Istimna’i kalma ce ta Larabci. A Hausa akan kira mummunar ɗabi’ar da zinar hannu ko auren hannu. A ɗan binciken da na yi, na fuskanci akwai ƙarancin bayanai da ke nuna illolin zinar hannu ga lafiyar jikin mutum.

Hakan ba zai rasa nasaba da rashin bincikenmu ba, mu baƙaƙe da kuma munafincin masu jajayen kunnuwa, saboda su na da wata manufa da suke muradin cimmawa. Kaɗan daga ciki su ne suna so su halasta auren jinsi. Sannan su na so kasuwar hada-hadar kayan istimna’i ta haɓayyafa. A wannan kasuwa ana siyar da sandararren zakarin roba irin na namiji, ana siyar da wanda mace za ta iya sarrafawa da hannunta sannan kuma ana siyar da mai aiki da kansa.

Abin tsoron shi ne sun ƙirƙiri sandarren gunkin roba na namji da na mace, wanda mutum zai iya siya ya tafi da shi gida. Duk lokacin da ya yi sha’awa ko ta yi sha'awa sai kawai su sadu da wannan gunkin roba. Tab! Wato akwai ƙura!

Su na ta cewa, yin auren hannu ba shi da matsala, wai ya na taimaka wa ɗan adam sanin zurfi da faɗin sha’awarsa. Sai dai kuma hakan ya ci karo da ƙorafin da al'umma ke yi akan illoli da matsaloli da suka fuskanta a sakamakon aikata wannan aiki a zahiri.

Ku biyo ni domin jin irin waɗannan matsaloli da zan kalla na yi bayaninsu a mahangar kimiyyar lafiya a rubutu na gaba da yardar Sarkin halitta.

Illarsa ga fata da gashi:

Yawan aikata istimna’i na da illa ga fata da kuma gashi. A lokacin saduwa, namiji da mace dukkansu su na fitar da ruwa da yake mai santsi, domin rage jin zafi gogayya (friction) tsakanin fatar zakarin namiji da fatar farjin mace; shi kuwa auren hannu ba shi da wannan. Mutum ɗaya ne kaɗai ke wasa da gabansa ko gabanta.

Duk da cewa, ko mutum ɗaya ne akwai ruwa da ya ke fita, ko kuma wasu za su ce ai su na shafa mai, domin cimma sauƙin wannan gogayya tsakanin hannunsu da gabansu, to tsuguno ba ta ƙare ba, tun da an keta yadda Sarkin Halitta ya tsara.

Wannan yawan guga da ake yi wa kafar farji ko azzakari zai iya sanya fatar wajen ta siɗe, ta yi ja ko ta dinga ƙaiƙayi ko ta yi ƙuraje; ya danganta da yawan aikata abin, wato sau nawa mutum ya ke yi a rana ko a sati.

Haka kuma idan mace tana amfani da kowanne irin mai wajen cimma wannan manufa, cuɗanyar man da halittun da ke matucinta kan iya jawo sabuwar matsala. Misali; wani nazarin masana a ƙasar Ghana ya nuna cewa, mata masu yin istimna’i da zakarin roba suna cikin haɗari, saboda sinadarin da aka haɗa shi na kemikal ne mai suna ‘phthalatic acid’. Yawan amfani da shi zai iya haifar da matsala. 

Haka kuma yawan yin istimna’i yana da alaƙa da zubewar gashi, saboda akwai wani sinadari a jikin mutum wanda ake tsarto shi da yawa cikin jini. Idan ya yi yawa a cikin jini sai ya kurɗa ya tafi inda jijiyoyin gashi su ke ya ɗamfare da su. Ta haka zai hana gashi miƙewa da girma, wanda a ƙarshe gashin zai karye. Faruwar hakan a jijiyoyin gashi da yawa shi ke kawo zubewar gashi. 

Idan haka ya faru a kan mutum, zai iya jawo ma sa sanƙo!

A mata ma su yi, su kan fuskanci zubewar gashin kai, na hammata ko na gaba. Maza kuma ya kan jawo musu zubewa ko karyewar gemu ko ƙasumba. Amma jiki iri-iri ne, jikinmu ya bambanta, kamar yadda fuskokinmu suka bambanta. 

Illarsa ga al’aura:

ɗaukar tsawon lokaci ana aikata istimna’i na da haɗari ga al’aurar maza da ta mata. Bari mu fara da illolin da ke shafar al’ aurar maza. Mafi yawan mazan da su ka mayar da wannan aika-aika ɗabi’ar su na wayar gari da matsaloli kamar haka: 

1. Raunin mazakuta ta yadda namiji ba zai iya samun ƙarfin gamsar da mace ba. Yawan yin istimna’i shi ne ke gajiyar da hanyoyin jinin da ke kawo wa mazakuta jini. A ƙa’ ida, waɗannan hanyoyin jini su na shikawa ta yadda idan namiji ya shiga sha’awa, yawan jinin da ke shiga cikinsu zai ƙaru, hakan shi ne ke sa gaban ya miƙe. Yawan aikata istimna’i yana sa wa hanyoyin jinin su gaji ta yadda ba za su shika da kyau ba, domin isasshen jini ya kai ga mazakuta. A sakamakon haka, sai a samu raunin gaba.

2. Saurin inzali: fFitar maniyyi kafin lokacin da ya kamata a ce ya fita. Galibi idan namiji ya na aikata wannan abu, to manufarsa ita ce ya gamsar da kansa, ba ya tunanin gamsar da matarsa tunda shi kaɗai yake yi. Matsalar ita ce zai sabawar kansa kawowa da wuri domin kawai ya gamsar da kansa. Idan ya saba da hakan, to zai iya samun matsala ta saurin inzali yayin saduwa, wanda hakan naƙasu ne ga rayuwar aure, saboda zai gaza wajen gamsar da matarsa.

A na can a na ta muhawara akan cewa ko yawan istimna’i zai iya haifar da ciwon daji (ga wata gujiya da ke taimakawa wajen samar da ruwan maniyyi) ko kuwa ba zai haifar da ciwon daji ba! Ku tara a rubutu na gaba. 

Illolin da zai iya haifarwa ga jijiya: 

Abinda na sani shine duk wata jijiyar da ta ke tsarto ruwa a jikin ɗan adam tana tsira ne daga barazanar ciwon daji (kansa) matuƙar ta na tsarto da ruwan da Allah ya tsara ta fitar.

Misali; akwai halittu a cikin maman mace da suke da alhakin samar da ruwan nono. Macen da ba ta taɓa shayarwa ba, ta fi shiga haɗarin kamuwa da kansar mama fiye da wadda ta taɓa shayarwa; namiji da yake fitar da maniyyi daga lokaci zuwa lokaci ya fi aminta da kuɓuta daga kansar maraina (prostate) fiye da wanda ya tara maniyyi bai fitar da shi ba. 

Amma a yadda na fuskanta a nazarin da na ke yi, akwai wata ɓoyayyiyar alaƙa tsakanin kansar maraina da yawan istimna’i. Wataƙila nan gaba idan bincike ya yi nisa a gano gaskiyar lamari. Wannan hasashe ne kawai, saboda ana can ana tafka muhawara akan wannan.

Illarsa ga mace:

A ɓangaren mata kuwa, shigar da sandararrun abubuwa domin gamsar da kai yana da haɗarin kawo shigar ƙwayar cuta (infection), wanda abu ne mai wahalar sha’ani sosai. Idan ana amfani da kayan itatuwa irinsu ayaba ko kokomba ko karas, musamman idan ba a wanke su da kyau ba, to sinadarin da manoma suka fesa musu ko kuma dattin ƙasar wajen da aka girbe su za su iya maƙalewa a jikin ɓawonsu. Idan aka yi istimna’i da su kuwa sai a samu shigar ƙwayar cuta.

Yawan amfani da abubuwa domin gamsar da kai zai iya sa wa gaban mace ya daina jin daɗin mazakutar namiji. Irin waɗannan mata namiji ba zai taɓa gamsar da su ba, saboda gamsuwar da su ke samu da istimna’i ya ninka gamsuwar da suke samu daga namiji. Sun sabar wa gabansu shigar sandararrun abubuwa a maimakon zakarin namiji, kamar yadda Sarkin Halitta ya tsara. 

Haka kuma bincike ya nuna yawan durza ɗan tsaka (clitoris) ya na lalata wayarin (nerɓe supply) da Allah ya yi masa. Ita wannan halitta tana saman ƙofar shiga gaban mace, kuma ta na jin taɓi sosai fiye da ko’ina kaf a jikin mace (the most sensitiɓe part of the female body). Idan aka lalata shi ta hanyar da ba ta dace ba, to babu shakka ƙarfin gamsuwa da za a samu daga saduwa zai ragu sosai da sosai.

Naku MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

©MIAbdullahi 2024