Wata ’yar sanda a Jihar Edo, Sufeto Edith Uduma, ta yi barazanar kashe kanta da ‘ya’yanta biyo bayan korar da aka yi mata daga aikin ’yan sanda bayan ta fallasa wani laifin fyaɗe da ake zargin wani abokin aikinta da aikatawa.
Ta zargi rundunar ‘yan sandan jihar da yi mata rashin adalci, inda ta ce jama’a ma ba su ji ta bakinta ba.
Korar Uduma ta zo ne bayan wani faifan bidiyo da ta ɗauka a watan Oktoba ya nuna wani Sajan Abraham, wani jami’in tsaro, rungume da wata yarinya ‘yar shekara 17 a ofishin ‘yan sanda da ke yankin Kudancin Ibie na jihar Edo.
An ga jami’in cikin gaggawa sanye da gejeran wando yana tambayar dalilin da ya sa Edith ke ɗaukar bidiyo. Ana cikin haka ne aka hangi yarinyar tana kwance akan kujera a wani ofishi.
An samu labari daga ’yan sanda cewa daga baya an sallami jami’an biyu bayan an gudanar da bincike.
Rundunar ’yan sandan jihar Edo a cikin wata sanarwa da ta fitar a watan Nuwamba ta hannun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Moses Yamu, ta yi zargin cewa Uduma ta haɗa baki da mijinta, Sufeto Ibrahim Mohammed, wajen karɓar miliyan N1 daga Abraham don ɓoye lamarin. A lokacin da aka ce Abraham ya bayar da Naira 45,000 a maimakon haka, an yaɗa bidiyon a yanar gizo, inji ’yan sanda.
Rundunar ’_yan sandan ta ce, “Hakan, sabanin rahotanni daga wasu sassan, ‘yar sandan ta ce, Edith Uduma, ita ce Jami’iyar da ke bakin aiki a ranar 7 ga Oktoba, 2024, da daddare a yayin da Sajan Abraham ya yi wa wata yarinya mata fyaɗe.
“Jami’iyar mace maimakon ta kai rahoton faruwar lamarin ga jami’in ‘yan sanda na shiyya ko kuma jami’in kula da abin da ya faru kamar yadda lamarin ya kasance, don a fara ɗaukar matakin ladabtarwa a kan jami’in da ya aikata laifin, sai ta yi amfani da damar wajen arzurta kanta ta hanyar kiran mijinta, Ibrahim Mohammed, wanda ta haɗa baki da shi don neman kuɗi miliyan N1m ba bisa ƙa’ida ba daga hannun Sajan ɗin domin ɓoye lamarin.
“Bayan waɗannan abubuwan, an fara shari’ar bisa tsari a kan dukkan jami’an, wanda ya kai ga korar Sajan Ibrahim da Edith Uduma.”
An kuma rage wa mijin Uduma matsayi zuwa Sajan.
Sai dai Uduma ta musanta zargin a wata hira da manema labarai, inda ta ce ba ta taɓa karɓar kuɗi ba, kuma ba a yi mata adalci ba. Ta yi zargin cewa an shirya korar ta ne saboda an tsane ta.
Uduma wacce ta yi barazanar kashe kanta idan ba ta samu adalci ba ta ce, “Abin da rundunar Edo ke faɗa ba abin da ya faru ba ne. Sun san ba ni da wani matsayi ko goyon baya da zan yi yaƙi da su, shi ya sa suka min haka,” in ji Uduma.
Ta kuma bayyana cewa hedikwatar rundunar da ke Abuja tana ci gaba da bincike kan lamarin sai dai rundunar Edo ta yi gaggawar sallamar ta.
“Ina son adalci. Korar da aka yi min ba adalci ba ne,” ta faɗa cikin kuka.
Ta ce mijin nata wanda shi ma aka sanya wa takunkumi ba shi da alaƙa da lamarin.