Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Uwargidan Shugaban Nijeriya, Aisha Muhammadu Buhari ta wallafa wani saƙo a shafinta na Facebook inda a ciki ta yi wa al’ummar Jihar Zamfara taddu’ar zaman lafiya.
Aisha Buhari ta wallafa saƙon ne da misalin ƙarfe 12:09 na daren Laraba, inda ta roƙi Allah ya samar wa mutanen jihar da sauran ‘yan ƙasar mafita daga matsalar tsaron da ta addabe ta, musamman a lokacin da Musulmi ke raya dare domin neman falalar Lailatul Ƙadri:
“Allah ya fitar da mu da mutanen Jihar Zamfara daga chikin wannan hali, albarkacin daren Lailatul Ƙadri, Ameen!”
Baya ga saƙon, uwargidan Shugaban Nijeriyar ta kuma wallafa wani saƙo na sauti mai tsawon minti 3:53, wanda a ciki ana iya jin wani mutumin da bai faɗi sunansa ba yana sanar da wani mutumin da ya kira ‘Haji Abdurrahman’ labarin wani kamun da ‘yan sa-kai suka yi wa wasu ɓarayin daji a yankin Tsafe da Mada na jihar Zamfara.
A farkon sautin ana iya jin muryar wata mata da ke cewa, “ga shi ku ji me yake faɗa…” Sai dai ba mu san ko muryar ta uwargidan Shugaba Buhari ba ce.
