
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ce bai shigar da wata sabuwar ƙara ba akan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
A wata sanarwa da mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Jackson Udom ya fitar, Akpabio ya bayyana cewa batun ya shigar da ƙarar neman biyan sa biliyan N200 akan Natasha ba gaskiya ba ne, abu ne da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma.
“Ikirarinta cewa an shigar da ƙarar, ba gaskiya ba ne, ruɗarwa ne, kuma da nufin rikita tunanin jama’a akan al’amarin”, inji Udom a sanarwar, ranar Lahadi.
Ya ce, an shigar da ƙarar ne tun tsawon sama da watanni uku da suka gabata, saidai an yi ta samun jinkiri akan hanyoyin gudanar da shari’a da wasu ƙa’idoji masu muhimmanci a kai.
Haka kuma ya bayyana cewa kotu ta yi ta ƙoƙarin gabatarwa Natasha ababen da ake tuhumar ta da su a kai, wanda a kodayaushe aka yi yunƙurin haka, sai ta kauce, lamarin da ya sa a watan Nuwamba kotu ta nemi mafita akan yin shari’ar ta wata hanya.
Shugaban majalisar ya jaddada cewa rikicin shari’a ana warware su ne a kotuna ba ta shirya zantuka da kumfar baki a kafafen Soshiyal Mediya ba.
Ya ƙara da cewa, yanzu ne lokacin da ya dace ta gabatar da hujjojin da ta yi ikirari a gaban kotu domin tabbatar da haƙiƙanin abinda ta ke zargin sa a kai ba neman tausayawa ko rufa-rufa ga asalin abin da suka tabbata ba.
